Kocin kungiyar kwallon kafa ta Sheriff Tiraspol Yuriy Vernydub wanda ya kafa wani babban tarihi a gasar zakarun nahiyaar Turai ta wajen doke Real Madrid ya koma kasarsa Ukraine don ya dauki makami wajen yaki da mamayar da Rasha ta yi mata.
Ya ce da karfe 4 da rabi na asuba dansa ya kira shi yana fada mai cewa ‘Rasha ta kawo mana hari’, yana mai cewa daga nan ne ‘na san cewa dole in koma gida’.
Vernydub yana daya daga cikin fitattun ‘yan wasan motsa jiki, ciki har da zakaran damben boksin na duniya Oleksandr Usyk, da suka koma gida don taiamaka wa kasarsu a wannan yaki.
Vernydub, wanda Rasha ya karkare sanarsa ta tamaula a kungiyar Zenit Saint Petersburg, ya shafe sa’o’i 11 a kan hanyarsa ta komawa gida a Asabar.
A wani labarin na daban Attajirin kasar Rasha Roman Abramovich, ya tabbatar da cewa ya yanke shawarar sayar da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, shekaru 19 bayan mallakarta.
Abramovich mai shekaru 55 da haihuwa ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, sayar Chelsea shi ne mataki mafi dacewa da zai amfani kungiyar mai rike da kofin gasar zakarun Turai.
Wannan kuwa nada nasaba da mamayar da Rasha ta yi Ukraine, yayin da ake kallon Abramovich a matsayin daya daga cikin na hannun daman shuganan Rasha Vladimir Putin.
Attajirin na Rasha ya kara da cewar, ba zai nemi kungiyar ta biya shi bashin da ya bata na fam biliyan 1.5 kwatankwacin dala biliyan 2.
Tun daga karshen makon jiya ne dai makomar Roman Abramovich a matsayin mamallakin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ke cikin barazana bayan wani attajirin Swizerland ya yi ikirarin cewa, tuni aka yi masa tayin sayen kungiyar ta Chelsea.
Biloniyan attaijirin mai suna Hansjorg Wyss ya shaida wa Jaridar Blick cewa, Abramovich na son raba gari da Chelsea cikin gaggawa bayan yin barazanar lafta masa jerin takunkumai a majalisar dokokin Ingila.
Tuni ma dai Abramovich din ya mika ragamar kungiyar ta Chelsea ga wasu mambobin kwamitin amintattu na kungiyar domin ci gaba da kula da ita.