A wani labarin na daban cibiyar kula da binciken kimiyyar zurfin teku da ayyukan injiniya ta kasar Sin ko IDSSE, wadda ke karkashin cibiyar nazarin kimiyya ta kasar Sin, ta ce na’urar nutso cikin teku mai zurfi ta kasar Sin ko ROV, ta kammala nutson mita 4,308 a tekun kudancin Sin.
IDSSE wadda ta bayyana hakan a ranar Alhamis, ta ce an yi dakon na’urar ROV da jirgin ruwan dakon na “Exploration-2”, kuma na’urar ROV ta gudanar da ayyuka yadda ya kamata bisa ingancin kirar ta, wanda hakan ya nuna na’urar na da ikon gudanar da binciken kimiyya da injiniyanci a karkashin teku mai zurfi.
Ana sa ran ROV kirar kasar Sin, za ta rika samar da damammakin mika bayanai ga na’ura mai kwakwalwa a fannin lantarki, da sadarwa, da sarrafawa, ta yadda za a iya ci gaba da amfani da ita wajen gudanar da ayyuka masu yawa, da suka shafi binciken kimiyya. (Saminu Alhassan).
Source:Legithausa