Sojojin India sun harba makami mai linzami cikin makwabciyarsu Pakistan a bisa kuskure, abinda ma’aikatar tsaron kasar Indian ta bayyana takaici akai.
Ma’aikatar tsaron India ta ce an samu kuskuren ne, a yayin da ake gudanar da aikin kulawa na yau da kullum ga makaman kasar, inda aka fuskanci tangardar na’ura da ta kai ga harba makami mai linzami cikin bazata cikin Pakistan a ranar Laraba.
Iyakar da suke tsakanin kasashen biyu dai na da dimbin sojojin bangarorin biyu, kuma an yi ta samun tashe-tashen hankula sau da dama a tsakaninsu, inda a wasu lokuta ake fargabar barkewar kazamin yaki da makaman nukiliya.
India ta sha zargin Pakistan da goyon bayan masu tayar da kayar baya, abinda ya sanya jiragen yakinta yin ruwan bama-bamai a wani sansani da tace na horas da ‘yan ta’adda ne cikin Pakistan a shekarar 2019, bayan wani harin kunar bakin wake da wata kungiyar gwagwarmaya ta Pakistan ta yi ikirarin kaiwa inda ta kashe sojojin India 40.
A wanai labarin na daban Firaministan India Narendra Modi ya ce su na da karfin iya murkushe Pakistan cikin kwanaki 10 muddin yaki ya barke tsakanin kasashen biyu da ke makwaftaka da juna.
A nata martani, Pakistan ta bayyana kalaman Firaminista Modi a matsayin rashin hankali daga mai bukatar yaki.
Tarihi ya nuna cewar kasashen India da Pakistan sun gwabza yaki sau 3 a shekarar 1947 da 1965 da 1971, bayan tashin hankalin da suka samu a tsakanin su a shekarar 1999.