Tawagar kwallon kafar Senegal na shirin doka wasanta na yau karkashin gasar cin kofin Afrika da ke gudana a Kamaru ba tare da ‘yan wasanta Kalidou Koulibaly da mai tsaron ragarta Edouard Mendy ba, wadanda suka harbu da corona gabanin wasan farko.
Teranga Lions wadda ta kai wasan karshe a gasar da ta gabata a 2019 kafin shan kaye hannun Algeria a Masar, na shirin haduwa da Zimbabwe ne anjima da yamma karkashin rukuninsu na B.
Rashin mai tsaron raga Mendy da mai tsaron baya Koulibaly da kuma Famara Diedhiou wadanda yanzu haka ke killace babban kalubale ne ga Senegal wadda za ta kammala wasannin gasar ba tare da Ima’ila Sarr ba wanda kungiyarsa Watford ta hana shi damar wakiltar kasarsa.
Sai dai duk da wannan kalubale mai horar da tawagar ta Teranga Lions, Aliou Cisse wanda ya amsa cewa suna cike da kalubale ya ce zasu shiga wasan cike da kwarin gwiwa iya yin nasara kan Zimbabwe.
Senegal wadda ke matsayin lamba 1 fagen tamaula a Afrika bisa jadawalin FIFA, ta na cikin jerin tawagogin da ake yiwa hasashen iya lashe kofin na Afrika bayan subuce mata a 2019.
A wani labarin na daban Zakaran kwallon Tennis na Duniya Novak Djokovic ya yi nasara gaban kotu game da karar da ya shigar kan hana shi damar haskawa a gasar Australian Open da hukumomin Australia suka yi baya ga tsare shi a hannun hukumar kula da shige da ficen kasar.
Hukuncin ya bukaci gaggauta sakin zakaran na Tennis lamba daya tare da bashi damar haskawa a gasar wadda za ta faro cikin watan nan.
Sai dai duk da hukuncin kotun lauyan gwamnati Chrisopher Tran ya ce za su amfani da karfin ikon da suke da shi wajen haramtawa Djokovic damar shiga kasar har na shekaru 3.
Matakin tsare Novak Djokovic dan Serbia mai shekaru 34 dai ya haddasa cece-kuce tare da kakkarfar zanga-zangar magoya bayansa musamman a kasarsa da kuma Australia wadan ke kiraye-kirayen bukatar sakin shi.
Tun farko hukumomin Australia suka sahalewa Djokovic damar shiga kasar tare da bashi Visa duk da kasancewarsa wanda ya yi fama da coronavirus a baya ba kuma tare da karbar rigakafin cutar ba, amma kuma bayan isarsa aka damkeshi saboda gaza nuna shaidar allurar.
Za dai a faro gasar ta Australian Open a ranar 17 ga watan nan.