Mutane a Najeriya sun fara gajiya da yadda farashin abubuwa musamman abinci ke kara hauhawa a kullun.
Bidiyon wani dan Najeriya ya yadu inda ya koka kan yadda farashin biredi ya yi tashin gwauron zabi Ta kai har mutumin ya furta cewa yadda abubuwa suke a yanzu, mutane sun kusa fara cinye junansu.
Wani mutumin Najeriya ya je shafin soshiyal midiya don kokawa a kan yadda farashin biredi ke tashin gwauron zabi a kasar.
A wani bidiyo da mutumin ya yi a cikin wani shagon siyar da biredi wanda shafin LIB ya wallafa, an gano yana korafi cewa sinkin biredi da ake siyarwa kan N300 ya zama N800 a yanzu.
Ya kuma bayyana cewa yadda abubuwa suka koma a yanzu, Mutane a Najeriya sun kusa fara yin kalaci da junansu.
“Na siya wannan biredin a watan da ya gabata N550, sai suka fara siyar da shi N600 yan makonni da suka gabata, yanzu kuma N800 ne. N800 fa kudin biredin da ake siyarwa N250 ko N300.
Ni kadai ina iya cinye wannan biredin ina ga mutum mai yara hudu.
“A haka ne wasu mutane zasu je gefe suna goyon bayan shirme, ku kalla yadda abubuwa ke tafiya a yanzu, lokaci zai zo da yan Najeriya za su fara kalaci da junansu.”
Jama’ar sun yi martani luxury_hairsbyneche ta yi martani: “Biredin da muke siyasa #480 na siye shi kan 1100 da yamman nan.” chioma_gold15 ta ce: “Biredi yanzu na masu kudi ne, na siya yau #800″ nana.thriftcloset ta ce: Na gama da biredin #500 yau Allah mun tuba” Legit.ng ta tuntubi wasu mutane don jin yadda abun yake a wajensu.
Wani ma’aikacin gwamnati mai suna Mallam Abubakar ya ce abun babu sauki domin shi kansa biredin da yake siya #500 ya koma #700.
Ya ce: “Abun dai ba a cewa komai amma talaka na ganin jarabawa, a nan Landmark biredin #500 ya koma #700 kuma kada kace ko an kara girmansa ne, a’a yana nan yadda yake.”
A nashi bangaren, wani magidanci mai suna mallam Ibrahim Ndanusa ya ce shi ya kusa daina cin biredi a gidansa yadda abubuwa ke tafiya yanzu.
“Ai biredi na mai kudi ne, na fadawa matata zan dunga siyo dan filawa tana murzawa idan har dole sai an ci din, amma abun ba sauki.”
A wani labarin, shahararren mawakin nan na siyasa kuma shugaban mawakan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Dauda Kahutu Rarara ya gudanar da wani taron addu’a na musamman.
Source:hausalegitng