Ana sa ran matatar mai ta dangote wacce za ta tace ganga 650,000 a kowace rana za ta fara aiki, inda kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) zai dinga jigilar danyen mai har jirgin ruwa shida zuwa ga matatar a watan gobe.
Jigilar man zuwa Matatar zai kara kaimi wajen tabbatar da inganci wajen gwajin matatar kamar yadda majiyoyi Uku daga masana’antar da ke da masaniya kan shirin suka shaida wa LEADERSHIP.
Matatar wacce hamshakin attajirin Afrika, Aliko Dangote ya dauki nauyinta, za ta sauya tsarin kasuwancin mai a Tekun Atlantika, inda ake kyautata tsammanin zama kishiya ga sauran takwarorinta na Turai da Amurka da ke kasuwancin na tsawon shekaru a yankin.
A wani labarin na daban hukumar kula da asusun taimakekeniyar kiwon lafiya ta jihar Bauchi (BASHCMA), ta kimtsa domin shigar da mutum miliyan biyu cikin tsari domin su samu cin gajiya, hakan, wani mataki ne na kyautata kiwon lafiya a tsakanin jama’a musamman masu fama da matsatsin tattalin arziki.
Wakilinmu ya labarto cewa, shirin na da manufar taimaka wa kiwon lafiyan mutane da ke da ƙaramin ƙarfi musamman ‘yan kasuwa, manoma, da sauran masu gudanar da ƙananan sana’o’i.
Babban sakataren hukumar, Dakta Mansur Dada, shi ne ya shaida hakan lokacin da yake ƙaddamar da kwamitin mutum 34 da aka ɗaura wa alhakin shigar da mutanen cikin shirin a ofishinsa.
Kwamitin ya haɗa da ma’aikatan BASHCMA, jami’an kula da shirin a ƙananan hukumomi 20, haɗi da sauran jami’an da lamarin ya shafa da ake sa ran za su faɗaɗa shiri ta yadda jama’a za su samu sauƙin shiga a dama da su domin cin gajiyar shirin.
Dada, ya kuma yi fatan cewa za a samu asalin talakawan da sdaa dace su shiga shirin ta hanyar wayar da kai da faɗakar da su muhimmancin shiga tsarin domin kyautata kiwon lafiya.
Dada ya ƙara da cewa, kwamitin na da damar tuntuɓar masu ruwa da tsaki a ƙananan hukumomi domin tabbatar da inganci gami da tabbatar da inganta kiwon lafiya yadda ya dace.
Source: LEADERSHIPHAUSA