Shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai bar wa gwamnati mai zuwa nauyin bashin da ya kai har na Naira tiriliyan 46.25.
Ofishin da ke kula ba bibiyar bashin kasar nan DMO ya bayyana cewa, jimlar bashin da ake bin Nijeriya, ya kai yawan Naira tiriliyan 46.25.
Kafar yada labarai ta Daily Post ta ruwaito cewa, duk da kurara da yawan dimbin bashin ya janyo, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa, ta samu karin amincewar ciwo wani bashin daga gun babban bankin duniya wanda ya kai Naira biliyan 369 kafin a cire tallafin man fetur a watan Juni na 2023.
A cikin shekaru takwas na gwamnatin Buhari, bashin da ake bin Nijeriya ya karu daga Naira tiriliya 12.6 a 2015 zuwa sama da Naira 46 tiriliyan a 2023.
Lamarin ya ci gaba da haifar da damuwa, musamman ganin cewa, Asusun bayar da lamuni IMF ya shelanta cewa, Nijeriya har ta kai matsayin taste Asusun ta wajen biyan bashi a 2022.
Hukumar tara haraji ta yi kasa FIRS ta sanar da cewa, ta karbo kudin shiga Naira tiriliyan 10 a 2022, inda kudin da aka kashe a cikin kasafin kudi na 2023 suka kai Naira tiriliyan 21.83,inda aka samu gibin da ya kai na Naira tiriliyan 11.34.
Maganar dorewar bashin da kuma dai-daita tattalin arzikin Nijeriya a yanzu, ya rikewa Nijeriya Wuya ba kuma tare da yin wani fata mai kyau ba.
A bisa maganar gaskiya, kalubalen da tattalin arzikin Nijeriya ya ke a ciki a yanzu, zai koma ne kachkam, a kan WuyanTinubu bayan an rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayun 2003.
Sai dai, kwararru a fannin tattalin arziki sun yi nuni da cewa, akwai jan aiki wajen dai daita bashin da ake bin Nijeriya.
Daya daga cikin kwarraun Farfesa Bongo Adi ya shefawa kafara Daily Post cewa, bashin da gwamnatin Buhari ta ciwo wa kasar nan ya jinginar da makomar kasar ta hanyar nauyin da suka hau kanta.
Adi wanda Farfsan koyar da darasin tsimi da tanadi ne a Business School da ke a jihar Legos ya bayyana hakan ne a ranar Litinin da ta wuce, inda ya ci gaba da cewa, a kwanuka masu zuwa, tattalin arzikin Nijeriya zai yi wuya ya saith, domin gwamnatin Buhari ta tafi, ta bar kasar babu kudi.
Ya yi nuni da cewa, mafia daya ce, kawai gwamnatin mai zuwa ta tattauna kan ciwo bashi wanda dama ko a fadin duniya, an amince da yin irin wannan, musamman don gwamnatin ta rike darajarta.
A cewarsa,“Akwai kuma wani karin bashin dala miliyan 800 da gwamnatin ta karbo daga gun bankin duniya, ba tare da sanin ta ya ya ne, za ta biya shi ba ”
Ya kara da cewa, sun yi amfani da damar ciwo bashin ne kawai don raba shi a tsakanin su ganin cewa, suna shirin barin gwamnatin domin sun san, babu wanda zai ce sai sun biya shi.
Ya ce, babu sauran wani abu da za a yi magana kan cewa, Nijeriya ta riga ta ciyace, domin kwanukan da ke tafe, ba za su yi wani dadi ba akai.
Ya ce, manyan Likitocin da sauran kwararru a sauran fannoni suna ta ficewa daga kasar nan, shin wanene zai kirkiro da hanyoyin da za a biya bashin? abubuwan da ake sa ran za su taimaka wajen farfado da tattalin arzikin Nijeriya, duk sun durkushe.
A cewarsa,“Suna ci gaba tara mana bashi wanda hakan zai jefa rayuwar mu a cikin matsala, inda hakan ke nuna kamarin zai fi na gobe muni.”
Ya ci gaba da cewa, za su mika mataccen tattalin arziki ga gwamnatin Tinubu ne kawai ban san irin sihirin da Tinubu zai yi don tafiyar da kasar ba.
Ya sanar da cewa, Bankin duniya bai taba baiwa Nijeriya ko wasu kaashe masu taso wa kan aikin da za su yi ba.
Ya bayyana cewa, babban abinda keda mahimmanci shine, a bai wa ‘yan Nijeriya kwarin guiwa don su ci gaba da zama a cikin kasar, amma kafin hakan ta kasance, dole ne sai an saita tattalin arzikin kasar da tabbatar da tsaro tukunna.
Ya ce, kowacce kasa na zuba jari ne akan matasanta, amma abin takaici, lamarin ba haka yake a Nijeriya ba. Shin ata yaya ne, tattalin arzikin kasar zai tunbatsa ?
Shi ma wani kwararre a fannin tattalin arziki Dakta Ayo Teriba ya sanar da cewa, kuskuren da gwamnatin Buhari ta yi shine, yawan ciwo bashi, inda ya yi nuni da cewa, dole gwamnatin mai zuwa ya koyi darasi don gujewa sake mai-maita irin ‘yar gidan jiya.
Source:LeadershipHausa