Kamar yadda gidan jaridar Leadership ta rawaito, ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta dakatar da fitar da Gas domin tabbatar da cewa farashin sa ya daina tashi a kasar.
Jaridar Leadership ta tattaro cewa, Farashin gas din girkin a wannan satin ya kai har N1,400 sakamakon yawan neman sa akeyi a kasuwa.
Wannan kari Wanda yayi yawa idan aka kwatanta da N500 tun shekarar 2018 ya sanya matsanaciyar damuwa gami da taraddudi a zukatan iyalai a fadin kasar duba da dama a kwai sauran matsaloli da ake fama da su.
Ministan man fetur Ekperikpe Ekpo ya tabbatar da dakatar da fitar da Gas din a wani taron karawa juna sani na cikin gida da aka gudanar a Abuja.
Ministan yace matakin na cikin kokarin samar da yawaitar Gas din girkin a kasuwannin cikin gida domin ragewa masu saye radadin tsadar sakamakon yawaitar neman gas din girkin.
Ekpo kuma ya tabbatar da cewar suna kuma tattaunawa da ‘yan kasuwa wadanda abin ya shafa, cikin wadanda ake tattaunawa da su har da Kamfanonin Mobil, Chevron da kuma Shell.
Yace tattaunawar ta maida hankali ne domin fustakar matsalolin da masu saye ke fama da su a dunkule, sa’annan a samawa kwamtomomin farashi mai sauki.
Ministan kuma ya nuna muhimmanci tsayar da fitar da Gas din girkin wanda ake sarrafa shi a cikin gida domin karkatar da shi ga masu amfani sa shi na cikin gida.
Ya kuma kara da cewa yin hakan yasa gwamnati tayi hasashen kara samun wadatuwar sa a kasuwanni cikin gida, wanda ake fatan hakan ya sauko da farashin kuma sakamakon hakan kwamtomomin dake fama da tashin farashi su samu sassauci.
See Also: Durkushewar Naira, Atiku Ya Bada Mafita
” A kwai fatan abubuwa zasu sauya, amma bama bukatar surutu a kan hakan, a ta bakin ministan.