Duk da naira biliyan 180 da tarayya ta bai wa jihohi don raba tallafin rage radadin kuncin rayuwa sakamakon cire tallafin mai, har yanzu ‘Yan Nijeriya na fama da kuncin rayuwa, bayan wata uku da bullo da shirin.
A ranar 17 ga wata Agusta 2023 gwamnatin tarayya ta sanar da raba wa jihohi 36 da babba birnin tarayya Abuja Naira biliyan 5 kowanne su amma shiru kake ji kamar an shuka dussa.
Bayani ya nuna cewa, kashi 52 na kudaden an basu ne a matsayin tallafi yayin da sauran kashi 48 na naira biliyan 5 din za su biya a cikin wata 20.
Tallafin na naira biliyan 5 ana sa ran ya rage radadin da al’umma suke ji sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi. Amma maimakon a samu sauki, sai dai korafi daga al’umma kan tsarin rabon tallafin yayin da su kuma jihohin ke karewa.
Misali, a JIhar Neja duk da kwamitin rabo da gwamnatin jihar ta kafa tun daga kananan hukumomi don raba kayan da aka sayo na Naira Biliyan 5.23, wadanda suka samu tallafin sun ce an ba su mudu daya ne na shinkafa da kwayoyin taliya da indomi wanda kuma ba yadda zai iya maganin radadin da ake fuskanta na janye tallafin mai.
Labarin yana da dan dadi daga Jihar Borno, don an fara bayar da tallafin tun daga watan Yuli, inda aka raba wa gidaje fiye da 400,000 a fadin jihar, an kuma fi bayar da muhimmanci ne ga wadanda yakin Boko Haram ya shafa.
Shugaban kungiyar nakasassu ta Jihar Borno, Ahmadu Umar, ya ce, wasu daga cikin manbobinsa sun amfana da rabon tallafin.
“Bayan wannan, wasu mambobinmu 2,000 na karbar tallafin naira 15,000 a wata daga gwamnatin jihar,” in ji Umar.
Ko a ‘yan makonnin da suka gabata, LEADERSHIP Hausa ta ruwaito yadda tallafin ya yi karanci a Jihar Kano inda wasu suka yi korafi sosai a kan tsarin rabon tallafin wanda wasu ma suka ce ba su gani a kasa ba
Labarin daya ne daga jihohin Delta, Benue Ekiti, an fitar da makudan kudade an sayi kayayyaki amma kuma abin da ya bai ga hannun talakawa ba.
Haka nan a Jihar Imo inda wasu da suka amfana suka ce, an ba su shinkafa cikin robar fenti abin da ba zai isa ya ciyar da iyali daya mai mutun hudu ba, sun ce maimakon tallafin ya rage radadi sai kawai ya kara tashin hankali na talaucin da ake fama da shi a kasa.
A Akwa Ibom, tuni aka dakatar da rabon tallafin bayan da aka fara raba buhu 40 na shinkafa ga kauye daya an kuma raba wa kauyuka 2,272 a kananan hukumomi 31 na jihar.
A Jihohin Kuros Ribas da Ribas da sauransu, wadanda suka amfana daga tallafin da aka raba sun koka a kan karancinsa.
Wani magidanci mazaunin kauyen Emago da ke karamar hukumar Abua/Odual a Jihar Ribas, Ennator James, ya bayyana cewa, buhun shinkafa daya aka ba al’ummarsu inda ake da mutum fiye da 700, “domin kowa ya samu sai muka raba wa kowa kofi daya na shinkafar ga duk mutum daya,” in ji shi.
Shirin bayar da bashin Naira Biliyan 275 ga masu kananan masa’anantu bai fara aiki ba.
Bayani ya juna cewa, har zuwa wannan lokacin shirin bayar da bashin Naira Biliyan 275 masu kananan masana’anantu da gwamnnati ta sanar bai fara aiki ba.
A watan Agusta ne Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da a fitar da a fitar da Naira Biliyan 275 don bayar da bashi ga masu manya da kananan masa’anantu, ya ce an yi haka ne don karfafa manya da kanana masa’anantun ta yadda za su samar da ayuyukan yi ga al’umma Nijeriya.
Ya kuma kara da cewa, gamnatin tarayya za ta kashe naira Biliyan 75 a stakanin watan Yuli 2023 zua watan Maris na 2024.
An shirya cewa, kowanne kamfani zai iya samun bashin naira biliyan 1 za a kuma biya bashin ne a cikin wata 60.
Amma kuma majiyar gwamnati na cewa har zuwa yanzu hukumar kula harkokin masa’anantu (SMEDAN) suna can suna aikin tantance wadanda za su amfana daga wannan tallafin.
Source: LEADERSHIPHAUSA