Wata mata mai suna Clarissa Rankin ta ajiye aikinta na koyarwa gami da komawa direbar motar daukar kaya inda take samun a kalla N64 miliyan duk shekara.
Matar,ta bayyana yadda mutane ke mamaki duk lokacin da suka ganta tana tuka babbar mota.
Hakan yasa tayi fice, yayin da a yanzu take da mabiya 1.8 miliyan a TikTok da masoya 105,000 a shafin Instagram a binciken da aka yi a ranar Talata, 20 ga watan Disamba.
Wata mata ta mayar da tuki wata sana’a mai ban sha’awa sannan tayi fice.
Matar mai suna Clarissa Rankin tana da tarin mabiya sama da 2 miliyan a TikTok da Instagram a binciken da akayi na ranar Talata, 20 ga watan Disamba.
Tun asali Clarissa ta karanta fannin shari’a na laifi daga bisani ta koma koyarwa, wanda take samun jimillar albashin N847,000 a shekara.
Sai dai, ta koma direbar babbar mota ne a lokacin da ta gane kudin da take samu daga aikin koyarwanta ba zai isheta rike iyalinta ba.
Yayin da ta fara tuka babbar motar, ta samu jimillar N22 miliyan a karshen shekara.
Kudin da take samu ya karu zuwa N64 miliyan duk karshen shekara lokacin da ta bude kamfaninta na JC Rankins Transport.
Clarissa ta bayyana yadda mutane a koda yaushe suke mamaki idan sun ganta kan motarta.
Ta sanar da CNBC cewa: “A koda yaushe mutane suna sawa a ransu direban babban mota a matsayin mutum mai katon ciki, tsoho mai gemu kuma mai sanya biri da wando.
“Ina jin dadin ganin alamar mamakin nan a fuskokin mutane irin, ‘Da gaske zaki iya tuka wannan?’ ni kuma sai ince, ‘Eh, hakan na matukar birgeni.”
Baya ga sana’arta na tuka babbar motar, tana samun karin N16 miliyan daga TikTok inda take da kusan mabiya 2 miliyan.
Clarissa ‘yar shekara 36, ita da yaranta da mijinta suna zaune ne a Chorlotte, arewacin Carolina.
Bidiyon Bakon Biki da ya Kaiwa Amarya da Ango kyautar itace A wani labari na daban, wani bako ya kaiwa amarya da ango gudumawar itace.
Amarya da angon sun matukar jin dadi inda cike da shewa suka tsaya suka dauak hoto tare da shi.