Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya janye umarnin da ya bayar ga dukkan bankunan kasuwanci a ranar 6 ga Mayun shekarar 2024, inda ya umarce su da su aiwatar da cire kaso 0.05 cikin 100 daga duk wata hada-hadar kuɗi ta banki a matsayin harajin tsaron yanar gizo.
Umarnin cazar harajin ya janyo cece-kuce a faɗin ƙasar nan a lokacin da babban bankin ya gabatar da ƙudirin a makon da ya gabata, lamarin da ya sa fadar shugaban ƙasa ta dakatar da aiwatar da karɓar harajin na intanet.
A wata sanarwar janye ƙudirin da CBN ya fitar a daren Lahadi, ya umurci bankunan da dakatar da bin umarnin farko, kamar yadda shugaban ƙasa ya buƙata, hakan alama ce da ke nuna cewa gwamnatin mai ci tana saurare tare da bada fifiko ga koken jama’a.
A wani labarin na daban mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya ƙaddamar da Shirin Inganta Ilimin Sakandare (ASSEP) wanda hukumar raya yankin Arewa maso Gabas (NEDC) ke aiwatarwa domin shawo kan matsalolin da suke shafan harkar ilimi a matakin sakandari musamman magance fita daga makarantar sakandare a shiyyar Arewa maso gabas.
Shirin ASSEP na da nufin inganta ilimi da koyar da sana’o’i ga ɗaliban da suka kammala karatun sakandare a faɗin jihohin Arewa Maso Gabas guda shida.
Da ya ke ƙaddamar da shirin a gidan gwamnatin jihar Bauchi ranar Asabar, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya jaddada muhimmiyar rawar da ilimin sakandare tamkar wani tsani bayan karatun firamare, yana mai bayyana ƙalubalen tarihin yankin na Arewa maso Gabas wajen aiwatar da tsare-tsaren ilimi bai ɗaya da kuma shawo kan ƙalubalen da al’adu ke yi ga ilimin boko.
Ya ce yankin na Arewa Maso Gabas yana fama da ƙarancin shigar yara makarantun sakandare, wadda kwata-kwata bai wuce kaso 19 cikin ɗari ake da shi ba, idan aka kwatanta da alƙaluman shiga yara makarantun sakandare a ƙasa, wadda ya kai kaso 39 cikin ɗari.
Shettima Shettima Shettima ya yabawa gwamnonin shiyyar bisa haɗin kai da jajircewarsu wajen inganta yankin, inda ya yaba da ƙoƙarinsu na ganin an haɗa kai don cike giɓi a harkokin mulki.
Manajan Daraktan hukumar ta NEDC, Mohammed G. Alkali ya yi ƙarin haske kan manufofin shirin na ASSEP, waɗanda suka haɗa da inganta makarantun gaba da sakandare, da bunƙasa sana’o’in hannu, da kuma inganta ƙwarewar malamai.
DUBA NAN: Hukumar Alhazai Ta Bayyana Lokacin Da Za’a Kammala Aikin Hajin Bana
Alkali ya jaddada aniyar shirin na mayar da hankali kan shirye-shiryen Kimiyya da Fasaha da Injiniyanci, da Lissafi wato (STEM) da kuma sadarwa, waɗanda ke da muhimmanci wajen bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire, da tunani mai zurfi a tsakanin matasa.