Sakamakon luguden wutar da su ka sha, mayakan ISWAP sun birne ‘yan uwansu guda 77 a wuraren Marte, kamar yadda rahotannin sirri su ka nuna bayan Sojojin sama sun dinga auna wa mayakan wuta ta jiragen sama inda su ka ratsa sansanayen mayakan guda uku da ke kusa da tafkin Chadi.
Lamarin ya auku ne a ranar 19 ga watan Disamban 2021 wanda jami’an tsaron hadin guiwa na kasashe karkashin Operation Hadin Kai su ka kai wa mayakan farmaki.
Bayan shan luguden wuta da ragargaza, mayakan ISWAP sun birne ‘yan uwansu guda 77 a wuraren yankin Marte, Daily Nigerian ta ruwaito.
Kamar yadda rahotanni daga PRNigeria su ka nuna, an halaka mayakan ne bayan farmaki da sojojin saman Najeriya su ka kai sansanayen ‘yan ta’addan guda uku da ke wuraren tafkin Chadi.
Bayan an samu bayanai akan yadda sojojin su ka lalata musu bindigogin yaki da babura da dama yayin farmakin.
An yi amfani da kayan yaki na ban mamaki wata majiyar sirri daga sojoji ta bayyana yadda yayin kai farmakin aka yi amfani da jiragen Super Tucano da sauransu wurin kai wa mayakan ISWAP din hari.
Kamar yadda majiyar ta shaida: “Hare-haren da sojojin sama, karkashin Operation Hadin Kai da taimakon jami’an tsaron hadin gwiwa na kasa da kasa (MNJTF), ya auku ne a ranar 19 ga watan Disamban 2021, a sansanayensu uku inda su ka halaka daruruwan ‘yan ta’adda a Arinna Sorro, Arinna Ciki da Arinna Maimasallaci da ke karamar hukumar Marte a jihar Borno.
“Bayan bincike da amfani da dabaru na sirri, sojojin sun kai farmaki wurin mayakan da su ka tsira daga harin baya wanda sojojin su ka kai Kusuma da Sigir.
“An samu bayanan sirri akan yawan ‘yan ta’addan da su ka koma sansanayen inda su ke kula da mayakan da aka ji wa raunuka a harin baya.
An samu bayanai akan yadda mayakan ISWAP din su ka koma yankin don boye baburansu a duhun daji.”