Kungiyar ASUU tace an maida mambobin ta manoma da direbobin motocin haya saboda wahala.
A ranar Talatar nan malamai masu koyarwa a jami’o’i suka koka a kan yadda aka tagayyarar da su Farfesa Adelaja Odukoya ya caccaki gwamnatin tarayya a kan biyan ‘yan majalisa albashin miliyoyi.
Kungiyar ASUU ta malaman jami’a ta bayyana cewa mafi yawan ‘ya ‘yanta sun zama manoma da direbobi domin rayuwa tayi masu wahala.
Jaridar Vanguard ta rahoto shugaban ASUU na yankin Legas, Adelaja Odukoya ya na cewa Sanatoci da ‘yan majalisa suna samun albashi mai tsoka.
A lokacin da ‘yan majalisa suke tashi da makudan kudi a kowane wata, Adelaja Odukoya yace gwamnatin tarayya ta bar malaman jami’a a tagayyare.
Odukoya ya yi wannan bayani ne a ranar Talata, 14 ga watan Disamba, 2021, lokacin da ya zanta da manema labarai a jami’ar gona ta FUNAAB a Ogun.
Malamin makarantar ya zargi gwamnati da zaluntar malamai a dalilin kin dabbaka yarjejeniyar 2020.
Albashin malamin jami’a N400, 000 ne Shugaban na ASUU yace a lokacin da ‘yan majalisa suke karbar tsakanin N1.3m zuwa N1.5m duk wata, Farfesoshi ba su samun abin da ya zarce N416, 000.
Haka zalika kungiyar tace babu abin da zai hana ta tafiya yajin-aikin da ta yi niyya, muddin gwamnatin Muhammadu Buhari ba ta biya mata bukatunta ba.
A cewar Malamin, duk Duniya babu malaman jami’an da ake yi wa karancin albashi irin na Najeriya.
“Albashinmu yanzu ba ya isanmu; Mun dade mu na cewa abubuwa sun yi tsada a kasar nan. Amma babu wanda yake cewa komai a Najeriya.”
“A kara albashin malamai ya zama matsala. A lokacin da Ahmad Lawan yace Sanata na karbar N1.5m, ‘yan majalisar wakilai na karbar N1.3m.”
“Za ku yi mamakin ku ji cewa mafi yawan da ke wajen Legas mu na yin kabu-kabu da sauran ayyuka domin albashinmu ya yi kadan.” – ASUU.
ASUU ta caccaki Ahmad Lawan Rahoton yace Adelaja Odukoya ya yi wannan magana ne a matsayin raddi ga shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, wanda ya koka game da alawus dinsu.
Kwanaki kungiyar ASUU ta malaman jami’a ta reshen Owerri, tayi barazanar garkame jami’o’i sai lokacin da Allah ya yi, idan suka shiga yajin aiki a shekarar nan.