Gwamnatin tarayya a ta bakin ministan mai ipre Sylva tace babu hannunta a karin farashin man fetur da aka yi a cikin watan Yuli Ministan harkokin mai na Najeriya.
Timipre Sylva ya zargi ‘yan kasuwa da kara kudi daga N165/lita Sylva a wajen wani taron NMDPRA ya tabbatar da cewa gwamnati na biyan tallafin fetur har yau.
A farkon makon nan aka ji Gwamnatin tarayya ta hakikance a kan cewa ba ta kara kudin litar man fetur daga N165 da mutane suka saba saye ba.
A ranar Litinin, 1 ga watan Agusta 2022, Punch tace gwamnati ta fito tana bayanin cewa ‘yan kasuwa ne suka kara farashi zuwa tsakanin N175 da N230.
Rahoton yace gwamnati ba ta bayyana abin da ya sa ta gagara tabbatar da farashin da ta tsaida ba.
Kwanakin baya ‘yan kasuwa suka yi nasarar daga farashin litar man fetur daga N165, canjin da aka samu wannan karo ya danganta daga yanki zuwa yanki.
Abin mamaki shi ne an yi wannan kari ne ba tare da amincewar gwamnati ba. Baya ga haka, har yanzu hukuma tana ikirarin tana da ta-cewa a kan harkar mai.
Su dai ‘yan kasuwa sun ce ba zai yiwu a saida litar man fetur a kan N165 a gidajen mai ba. Daga cikin dalilansu shi ne man fetur ya yi wahala a fadin Najeriya.
Da yake jawabi a wajen taron da hukumar Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority ta shirya, Timipre Sylva yace ba su canza farashi ba. Karamin Ministan harkokin man ya bayyana cewa har zuwa yau, ba a bar sha’anin mai a hannun ‘yan kasuwa ba, gwamnati ta na da ta-cewa kan tsaida farashi.
Bugu da kari Timipre Sylva yace gwamnatin tarayya ta na biyan tallafin fetur kamar yadda aka sani. Ministan yace idan ba hukuma tayi kari ba, zai zama ‘yan kasuwa ne. Hukumar NMDPRA za ta sa baki.
A wani rahoton, mun ji Ministan yana cewa zai tuntubi shugaban hukumar NMDPRA domin tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta yanke farashin da ya kamata.
Shugaban NMDPRA, Farouk Ahmed ya yi jawabi a wajen taron, yake cewa sashe na 216 na dokar PIA ya ba ‘yan kasuwa damar sa baki a kan batun farashin lita.
Man dizil ya tashi a kasuwa Wani ‘dan kasuwa ya shaidawa Legit.ng cewa suna kashe makudan kudi wajen jigilar fetur daga tashoshi zuwa gidajen mai saboda irin tsadar da dizil ya yi.
Manyan motoci na shan litar mai ne a kan kusan N800, wanda hakan ya jawo kudin dako ya tashi. Cigaba da saida fetur a N165 na nufin ‘yan kasuwa za suyi asara.
Source:hausalegitng