Kungiyar Kwadago ta Nijeriya NLC, za ta fara yajin aikin gargadi na kwanaki biyu daga ranar Talata 5 ga watan Satumba, domin nuna adawa da shirin gwamnatin tarayya na cire tallafin Man Fetur da gazawarta kan magance kalubalen da ke haifar da cire tallafin man fetur din.
A ranar 2 ga watan Agusta, ƙungiyoyin kwadago sun nuna rashin amincewa da kudurin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, kan cire tallafin.
Kungiyoyin kwadago a Nijeriya NLC da TUC da sun gudanar da zanga-zanga a babban birnin tarayya Abuja da jihohi da dama da suka hada da Legas, Abia, Plateau, Kaduna, Kano, Rivers, Zamfara, Katsina, Cross River. , Ebonyi, Enugu, Kwara, Ogun, Imo, Ondo da Edo.
Kungiyar ta NLC ta baiwa gwamnati wa’adin kwanaki bakwai, inda ta bukaci da a gaggauta sauya duk wasu kudurin gwamnatin tarayya na yaki da talauci da suka hada da karin farashin man fetur da aka yi a baya-bayan nan, da karin kudin makarantun gwamnati da batun shafe watanni takwas na hana albashin malaman jami’a hakkokinsu”.
Kungiyar ta kuma bukaci a sake duba mafi karancin albashi daga N30,000 zuwa N200,000, tana mai cewa tun lokacin da Shugaban kasa ya yi jawabi a ranar rantsar da shugaban kasa a ranar 29 ga Mayu, 2023 hankalin ‘yan Nijeriya ya tashi.
Source: LEADERSHIPHAUSA