Shehin Malami kuma babban masani a bangaren tattalin arziki (Economy), Farfesa Ahmad Sanda, da ke aiki a jami’ar Usmanu Danfodio da ke Sokoto a tsangayar koyar da nazarin tattalin arziki, ya shaida cewar, matsalar da matasa ke haifarwa ta zuwa rumbunan adana kayan abinci da fasawa domin kwashewa ko daka wasoso ga mo-tocin dakon kayan abinci ba za su shawo kan matsalolin matsin rayuwa da ake ciki ba illa ma kara jefa kasar cikin mayuwacin hali.
Ya shaida cewar, ana cikin mawuyacin halin da akwai bukatar gwamnatoci da masu ruwa da tsaki za su tashi tsaye domin jawo hankalin matasa da su kauce wa dabi’ar fasa wurare da sunan neman abinci.
An Rufe Taron Koli Na Kafofin Yada Labarai Dangane Da Kwaikwayon Hazikancin Dan Adam A Afrika
Kishi: ‘Yansanda Sun Cafke Ma’aikacin Lafiya Da Yunkurin Hallaka Ma’aurata A Bauchi
A cewarsa: “Wannan alama ce ta kamarin yunwa da tsadar rayuwa da ake ciki. Hanya mafi sauki ta shawo kan wannan matsalar shi ne gwamnati ta tabbatar duk wani kayan abinci da aka ware domin rabarwa a irin wannan yanayin ana kawowa a rabar ba wai a je a tara a ajiye a rumbu ba.
“Domin kwasan kayan abinci a kai rumbunan ajiye abinci mutane za su yi tunanin an ajiye ne domin a yi sama da fadi da su.
In so samu ne daga inda aka kawo abinci domin rabarwa kawai a kai su ga jama’a kai tsaye a tabbatar an rabar. Kai tun kafin ma su iso a yi tsarin da suka dace suna zuwa a mika ga jama’a.
A irin lokacin da talakawa ke matsin rayuwa gaskiya babu bukatar zuwa a ajiye abinci a boye.”
A cewarsa, akwai bukatar a tsaurara matakan tsaro domin fasa wuraren adana kayan abinci wata alama ce da ke nuni da cewa an tura mutane zuwa bango, don haka idan ba a dauki matakan tsaro ba, nan gaba sai an rasa wurin da za a ajiye wani abu da sunan abinci, “A daidai gabar daukan matakin tsaro gwamnati ta tabbatar tana raba wa jama’a abinci ba zuwa a boye ba.”
Dangane da masu daka wasoso kan kayan abinci a motocin dakon ‘yan kasuwa, bab-ban malamin ya ce, akwai fa babban matsala, yana mai cewa hakan ba zai yi komai ba illa kara jefa farashin kayayyaki domin ya yi tsada.
“Gaskiya wadannan matsalolin sun shafi wasu abubuwa da suka ma zarce sashin tat-talin arziki shi kadai. Domin babu wani bangare a bangaren tattalin arziki da ya bai wa jama’a damar daka wawa kan kayan mutane.
“Akwai bukatar masu ruwa da tsaki daga bangarori daban-daban su shigo cikin wan-nan matsalar, malamai su wayar da kai.
“Eh an sani idan mutane na cikin matsatsin rayuwa, mutane ba za su saurari wasu bayanan ba, amma ya kamata dukkanin masu ruwa da tsaki kowa ya fito ya tofa al-barkacin bakinsa da kuma yin abun da ya dace.
“Kuma yana da kyau a nusar da matasa illolin fasa kayan abincin mutane. Domin idan ana fasa kayayyakin mutane ba ma na gwamnati kadai ba har da na ‘yan kasuwa ka ga wannan ba cigaba zai kawo ba zai kara tabarbara tattalin arziki ne. domin hauhawar farashin kayayyaki da gwamnati ke kokarin ta ga ta shawo kansa abun zai ta’azzara.”
“Gwamnoni, shugabannin kananan malamai, limamai, fastoci, kungiyoyi, kowa da kowa da su fito su jawo hankalin matasa kan cewa daka wawa ga kayan jama’a ba shi ne mafita ga wannan matsalar ba, kuma ba zai haifar da da mai ido ba. Don a maima-kon a samu sassaucin kayayyaki to wasoso zai sa farashi ya kara yin sama ne.
DUBA NAN: Masar Tana Kokarin Taimakon Falasdinawa?
“Domin dan kasuwa ya sayo kayansa ya yi asararsu ka ga ba zai koma ba hakan zai sanya a samu karancin kayayyakin da har farashi zai kara hauhawa.”