Direbobin tankunan daukar mai zasu fara yajin aikin gama gari daga gobe litinin domin bayyana damuwar su dangane da lalacewar hanyoyin motan dake fadin kasar.
Aboyeji yace yajin aikin direbobin zai shafi kasa ne baki daya.
Jami’in yace sun dade suna bayyana shirin yajin aikin, amma suke dakatarwa saboda tunanin irin illar da zai haifarwa jama’a ‘yan kasa.
Shugaban kungiyar direbobin yace a halin da ake ciki yanzu, tankin mai kan kwashe kwanaki 5 zuwa 6 idan tayi dakon man daga Lagos zuwa Abuja saboda tabarbarewar hanyoyin, wanda ya bayyana shi a matsayin abin kunya ga Najeriya.
Aboyeji yace kokarin su na janyo hankalin hukumomin Najeriya akan lalacewar hanyoyin yaci tura.
‘Yan Najeriya sun dade suna korafi dangane da lalacewar hanyoyin motocin kasar, inda suke zargin gwamnati da rashin kula saboda yadda jami’an ta ke zirga zirga ta jiragen sama, yayin da talakawa ke shan ukuba.
Lalacewar hanyoyin na daya daga cikin abinda barayi da ‘Yan bindiga ke amfani da shi suna yiwa mutane fashi da kuma garkuwa da jama’a.
A wani labarin na daban sarkin Sokoto Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana matukar damuwa akan yajin aikin kungiyar likitocin Najeriya inda ya bukace su da su yiwa Allah su janye domin takaitawa Yan kasa wahalar da suke sha.
Sanarwar ta roki likitocin da suyi nazari akan rantsuwar aikin da suka yi da kuma illar da annobar korona keyi a kasa tare da cutar amai da gudawa wajen dakatar da yanzu haka ke hallaka rayuka wajjen janye yajin aikin.
Sarkin Musulmin ya kuma roki ministan kwadago da ya sake tunani akan matsayin gwamnati na dakatar da tattaunawar da suke da likitocin ganin irin illar da Yan Najeriya ke fuskanta.
Sanarwar ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta shiga tattaunawa ta gaskiya da shugabannin kungiyar likitocin ta hanyar da zata karfafa guiwa tsakanin bangarorin biyu, inda take cewa gwamnati na da alhakin shawo kan likitocin da kuma duba bukatun su ta hanyar da ta dace.
Sarkin Musulmin ya yabawa saka bakin da Majalisar dokoki tayi tare da wasu Yan Najeriyar da suka nuna damuwar su akan al’amarin, inda ya bukaci ma’aikatar lafiya da na kwadago da kuma likitocin da su koma teburin sasantawa.