Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan aware ne a kudu maso gabashin Najeriya sun kashe ‘yan sanda uku tare da raunata wasu biyu.
“Mun rasa jami’ai uku” sannan wasu biyu kuma sun samu raunuka, in ji shi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Daniel Ndukwe ya tabbatar da faruwar harin amma ya ki tabbatar da adadin wadanda suka mutu a dalilin harin ‘yan bindiga din.
“Yace har yanzu bamu da cikakken bayanai da suka shafi lamarin, amma an fara farautar ‘yan bindigar,”
A yankin Kudu maso Gabashin Najeriya dai ana fama da tashe-tashen hankula, inda a shekarar da ta gabata aka kashe ‘yan sanda da wasu jami’an tsaro sama da 130, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka bayyana.
Hukumomin kasar dai sun dora alhakin kai hare-hare a kan haramtacciyar kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra a yankin ‘yan kabilar Igbo, ko kuma reshenta da ke dauke da makamai da ake kira ESN.
Kungiyar dai ta musanta alhakin wannan tashin hankalin yankin.
A wani labarin na daban Kungiyar ba da agaji ta kasa da kasa Red Cross ta yi gargadin cewa tsarin kiwon lafiyar kasar Afghanistan yana gaf da durkushewa, sakamakon rufe cibiyoyin kiwon lafiya fiye da dubu 2,000 a duk fadin kasar da ke fama da rikici.
Daraktan kungiyar a yankin Asiya da Pacific, Alexander Matheou ya ce ma’aikata na iya jure aiki ba tare da albashi ba na ‘yan makwanni, to amma da zarar magunguna sun kare babu wani taimakon da za a iya bayarwa ga mara lafiya.
Kungiyar ta ce fiye da ma’aikatan lafiya dubu 20 ne suka daina aiki, ko kuma su ke aiki ba tare da albashi ba, kuma dubu 7 daga cikinsu mata ne.
Ko a makon da ya gabata, sai da hukumar lafiya ta duniya ta yi kashedin cewa kasa da rabin asibitocin da ke Afghanistan ne ke aiki, kuma hakan zai iya kawo cikas a yakin da ka da annobar Corona.
Bayan yaki da ta yi fama da shi na kusan shekaru 20, tattalin arzikin Afghanistan ya samu nakasu tun bayan da kungiyar Taliban ta dare karagar mulkin kasar a watan da ya gabata a tsakankanin takunkumai da kuma dakile taimakon da ke isa kasar daga waje.