Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya ce zai dandanawa PDP kudarta idan jita-jitar da ya ke ji na korarsa ya zama gaskiya.
Wike ya ce yana jiran wannan ranar ta zo, ya kara da cewa a lokacin ne shugabannin jam’iyyar za su gane ko shi wanene.
Gwamnan ya na jagorantar wasu gwamnoni hudu na jam’iyyar wurin neman a yi adalci da daidaito a shugabancin jam’iyyar.
Neysom Wike, gwamnan jihar Ribas ya wofintar da barazanar cewa za a kore shi daga jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP.
Gwamnan ya bayyana cewa zai mayar da martanin da ya dace idan aka kore shi daga jam’iyyyar, The Nation ta rahoto.
Ya sha alwashin zai nuna wa jam’iyyar ainihin halinsa idan aka kore shi daga jam’iyyar mai hamayya.
Wasu Gwamnoni Sun Kama Hanyar Ficewa Daga PDP?
Atiku Ya Yi Magana Track News ta rahoto cewa gwamna Wike ya yi jawabi ne a taron da aka yi don karrama gwamnonin G5 a Fatakwal, jihar Ribasa a ranar Juma’a 18 ga watan Nuwamba.
Abin da ke faruwa game da PDP/Nyesome Wike/Zaben 2023/Gwamnonin G5/Jihar Ribas Gwamnonin na G5 sun kushin Seyi Makinde na Oyo, Samuel Ortom na Jihar Benue, Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu, Okezie Ikpeazu na jihar Abia da Wike kansa.
Gwamnonin da suka yi wa jam’iyyar bore suna neman shugaban jam’iyyar na kasa Sanata Iyorchia Ayu ya yi murabus ne da sunan adalci da daidaito kafin su mara wa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasar jam’iyyar baya.
Wani sashi na jawabinsa ya ce: “Sun ce za su kore ni. Ina jiran ranar da za su kore ni.
Idan sun kore ni, zan barbada musu yaji. Za ka san cewa kaki na leda bane.”
A Sabuwar Ganawar Da Suka Yi Kan Rikicin PDP A kokarin warware rikicin jam’iyyar PDP, dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya sake ganawa da Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas Wata majiya da ta halarci taron ta fada wa Daily Trust cewa wasu hadiminan bangarorin biyu sun halarci taron.
An yi ganawar ne a gidan gwamnatin Ribas da ke Asokoro a Abuja a ranar Alhamis.
Source:Legithausa