Tsohon Gwamnan Jihar Anambra Peter Obi ya bayyana janyewar sa daga takarar shugabancin Najeriya a karkashin Jam’iyyar PDP da kuma ficewa daga cikin ta kasa da sa’oi 72 kafin gudanar da zaben fidda gwanin jam’iyyar.
Wasikar ta bayyana cewar Tsohon gwamnan ya gabatar da aniyar sa ta janyewa daga PDP kamar yadda doka ta tanada wajen shaidawa shugaban mazabar sa dake Agulu ta 2 a Anaocha ta Jihar Anambra daga ranar 20 ga watan Mayu, matakin da ya kawo karshen aniyar sa ta tsayawa takarar shugaban kasa a Jam’iyyar.
Tsohon gwamnan wanda ya bayyana aniyar sa ta bada gudumawa wajen gina kasa, yace halin da ake ciki yanzu ba zai bashi damar yin haka ba ta hanyar da ta dace, duk da yake babu abinda ya sauya a shirin sa na bada gudumawa wajen ceto Najeriya.
Sai dai Daraktan yakin neman zaben sa Doyin Okupe ya tabbatar da cewar Obi zai tsaya takaran zabe mai zuwa ba tare da bayyana jam’iyyar da zai koma ba.
A wani labarin mai kama da wannan sohon Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari ya jagoranci magoya bayan sa na Jam’iyyar APC dake mulkin Najeriya domin sauya sheka zuwa Jam’iyyar adawa ta PDP saboda abinda suka kira rashin adalcin da aka nuna musu.
Tsohon gwamna yace bayan matsalar da aka samu a Jihar Zamfara, sai kuma jam’iyyar su ta APC ta mikawa Gwamna Matawalle ragamar jagorancin ta lokacin da ya sauya sheka daga PDP zuwa cikin ta, matakin da ya nuna rashin la’akari da rawar da suka taka wajen killace ‘yayan jam’iyyar ta su wuri guda duk da matsalolin da suka fuskanta.
Yari yace lura da wannan da kuma rashin adalcin da aka yiwa magoya bayan su a matakai daban daban, sun yanke hukuncin sauya sheka zuwa jam’iyyar da za’a mutunta su.
Shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara, Kanar Bala Mande ya tabbatar da sauya shekar a taron masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar da akayi a Gusau.
Kanar Mande yace sun cimma matsaya a tsakanin su akan yadda za’a habaka Jam’iyyar wajen aiki tare da sabbin ‘yayan ta, yayin da ake shirin bikin karba su nan gaba kadan.