Jami’an tsaron Rasha sun tsare mutane kusan 100 a biranen kasar 35, bayan da suka tarwatsa masu zanga-zangar adawa da yakin da sojojin Rashan suka kaddamar kan Ukraine.
Zuwa yanzu kididdiga ta nuna cewar adadin masu zanga-zangar da aka tsare a Rasha ya kai kusan 100 tun daga ranar 24 ga Fabrairu, lokacin da Shugaba Vladimir Putin ya umarci sojoji su mamaye Ukraine.
A wani labarin na daban kuma Hungary ta ce ba za ta bai wa kasashen duniya damar kai wa Ukraine makaman da za ta yaki Rasha da su ta sararin samaniyar ta ba, bayan da kungiyar kasashen Turai ta ce za ta aikewa kasar makaman yaki.
Ministan ya ce sun dauki wannan mataki ne domin kare lafiyar jama’ar kasar su da ke gida da kuma wadanda ke zama a cikin kasar Ukraine.
Szijjarto ya ce ana iya amfani da safarar makaman wajen kai harin soji wanda ke iya yiwa jama’ar su illa.
Ministan ya ce babban abinda ke gaban su a wannan lokaci shi ne tabbatar da lafiyar kasar su da kuma jama’ar ta, saboda haka ba za su saka hannu a yakin da ke gudana a makociyar su ba.
Babban jami’in diflomasiyar kasashen Turai Josep Borrell ya ce za su bada euro miliyan 450 domin sayawa Ukraine makaman yakin da za a mika mata.