An yi musayar wuta tsakanin Sojoji a Kamaru da gungun ‘yan bindiga a Buea, babban birnin yankin Bamenda da ke fama da rikicin ‘yan aware, birnin da a yanzu haka yake karbar bakuncin tawagogin kwallon kafar kasashen Afirka da ke fafatawa a gasar AFCON.
Bayanai sun ce an kai hare-haren ne jim kadan bayan da tawagar ‘yan wasan Mali ta kammala atisaye, jami’ai kuma sun ba da tabbacin cewar tashin hankali ba yi tasiri akan atasayen ‘yan wasan ba, sai dai an ba da rahoton mutuwar mutum daya, koda yake ba a tabbatar da hakan ba a hukumance.
Gabanin fara gasar cin kofin kasashen Afirka ne dai, sojoji na‘yan aware suka sha alwashin hana gudanar wasanni a yankunansu ta hanyar kai hare-hare.
Buea shi ne babban birnin yankin Kudu maso Yamma, wanda ke da makwabtaka da yankin Arewa maso Yamma ke fama da tashe-tashen hankula tun shekara ta 2017, lokacin da masu fafutuka na yankin masu amfani da Turancin Ingilishi na anglophone suka ayyana ballewa daga kasar Kamaru da akasarin al’ummarta ke magana da Faransanci.
A wani labarin na daban Kelechi Iheanacho na Super Eagles ya cirewa Najeriya kitse a wuta a karawarta da Masar yau talata bayan kwallonsa da ta bai wa kasar ta yammacin Afrika nasara a wasanta na farko karkashin gasar cin kofin Afrika.
A minti na 30 da fara wasa ne tauraron na Leicester ya zurawa Super Eagles kwallonta wanda ya bai wa Najeriya damar zama jagorar rukuninta na D da maki 3.
Yayin wasan dai Salah kaftin din tawagar ta Masar ya fusata matuka bayan mai tsaron ragar Najeriya ya barar da kwallon da ya yi kokarin zurawa a mintuna gab da karkare wasa bayan komawa daga hutun rabin lokaci.
Iheanacho dai ya lashe kyautar gwarzon dan wasa na karawar ta Najeriya da Masar.
A haduwa 8 da Najeriya ta yi da Masar a tarihi, sau 4 Super Eagles na nasara kan Pharaohs yayinda ta yi canjaras sau biyu ita kuma ta yi nasara a wasa biyu.