Rahotanni daga jihar Kebbi da ke arewacin Najeriya sun ce, mutane da dama sun rasa rayukansu, ciki har da wasu 13 da aka banka wa wuta a cikin wani gida, bayan da ‘yan bindiga suka kai hari a wani gari a karamar hukumar Riba ta jihar Kebbi a ranar Juma’a.
Wata majiya ta ce bayan arangamar ce ‘yan bindigar suka huce fushinsu kan al’ummar yankin da suka bazama daji saboda firgici, inda suka kashe mutanen da ba a tantance adadinsu ba.
Wadanda suka yi hijira zuwa garin Onashi sun ce yanzu haka akwai gawarwakin ‘yan uwansu da ke kwance a dazuka, kuma babu halin zuwa dauko su saboda fargabar abin da ka iya faruwa.
A wani labarin na daban Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa akalla mutane 200 ‘yan bindiga sun kashe tare da raba wasu dubbai da muhallansu, yayin munanan hare-haren da suka kai cikin makon jiya a Jihar Zamfara da ke yankin arewa maso yammacin kasar.
A ranar Asabar din da ta gabata ne dai i, wasu mazauna yankunan da lamarin ya rutsa da su, suka shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, akalla mutane 140 ‘yan bindigar suka kashe a tsakanin ranakun Laraba zuwa Alhamis.
Ko da yake a na ta bangaren gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana adadin mamatan ne akan mutane 58, bayan da Sarkin Anka ya ce mutane 22 aka kashe a yankinsa, yayin da Sarkin Bukkuyum ya sanar da mutuwar wasu 36, alkaluman da kakakin gwamnatin Zamfara Zailani Bappa ya tabbatar a wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar Asabar.
Ranar Asabar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ya yi A-wadai da hare-haren ta’addancin a Zamfara, da ya bayyana a matsayin huce fushi kan wadanda basu ji ba basu gani ba, da ‘yan bindigar suka yi, saboda hare-haren da jami’an tsaron suka kaddamar akansu a baya bayan nan.
Wasu majiyoyi sun ce, daruruwan ‘yan ta’addan da suka kaddamar da munanan hare-haren, masu biyayya ne da kasurgumin dan fashin dajin nan Bello Turji, wadanda hare-haren jiragen yakin sojin Najeriya ya tilastawa tserewa daga sansanoninsu da ke dajin Fakai a karamar hukumar Shinkafi.