Shugaban APC reshen jihar Enugu, Ugo Agbalah, ya rasa ƙujerarsa, an kore shi daga jam’iyyar baki ɗaya.
Bayanai sun nuna cewa tuntuni ake tuhumar shugaban da rashin yin rijistar zama ɗan jam’iyya, lamarin da ake tafka mahawara a Kotu Mai bashi shawara kan harkokin watsa labarai ya yi fatali da lamarin, inda ya ce duk kanzon kurege ne.
An kori shugaban All Progressive Congress (APC) reshen jihar Enugu, Ugo Agbalah, daga jam’iyyar, kamar yadda Jaridar Leadership ta ruwaito.
Jam’iyyar APC a yankin da tsohon shugaban ya fito, gundumar Udi/Agbudu, ƙaramar hukumar Udi a jihar, ita ce ta sanar da matakin ranar Jummu’a da daddare.
Matakin na ƙunshe ne a wata takardar kora mai ɗauke da sa hannun shugaban APC na gundumar, Mista Aduma Ferdinand, da Sakatare Onyia Francis, wacce aka raba wa manema labarai da daren Jumu’a a Enugu.
Takardar ta kunshi cewa an ɗauki matakin dakatar da shugaban jam’iyya na jiha ne bisa gazawarsa na bayyana a gaban kwamitin ladabtarwa domin amsa tambayoyi kan tuhume-tuhumen da ake masa.
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa mambobin jam’iyyar APC a gundumar ne suka rubuta ƙorafi kan Agbalah, inda suka tuhume shi da rashin yin rijista zama cikakken ɗan jam’iyya a matakin gunduma.
Sauran tuhumar da ake masa sun haɗa da tafiyar da jam’iyyar ba kan turba ba, lamarin da suke ganin mai yuwuwa ya jawo wa jam’iyya rashin nasara a 2023 da kuma rashin zuwa tarukan gunduma, kana baya ba da tallafi. Shin ya samu labarin korarsa?
Yayin da aka nemi jin ta bakinsa, Mista Agballah, ya yi fatali da rahoton cewa an kore shi, inda ya bayyana cewa duk waɗan da suka kulla manaƙisar ba su ne sahihan shugabannin gunduma ba.
Adamu Ya yi wannan furucin ne ta bakin mai bashi shawari kan harkokin watsa labarai, Kenneth Oforma, inda ya yi zargin cewa mutanen da suke ikirarin shugabanni ne karya suke yi.
“Mutumin da ya rattaɓa hannu a matsayin shugaba ba shi ne ainihin shugaban gunduma ba, shugaban gundumar mu sunansa Chinedu Ezeago.”
A wani labarin kuma Sanata, Yan Majalisun Jiha da Jiga-Jigan PDP Sama da 500 Sun Fice Daga Jam’iyyar Jam’iyyar YPP reshen jihar Akwa Ibom ta bayyana ɗaruruwan shugabanni da jiga-jigan PDP da suka koma cikinta zuwa yanzu.
Shugaban kwamitin tattara bayanan masu sauya sheƙa, Usenobong Akpabio, ya ce YPP ta kama hanyar nasara a zaɓen 2023.
Source: LEGITHAUSA