Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC ta amince da wani tsarin da zai iya kaiwa ga matakin karin farashin man fetur duk kuwa da hauhawar farashin danyen man da kuma kalubalen da ke taka rawa a kasuwannin duniya.
Masana tattalin arziki sunce tuni kungiyar ta OPEC mai mabobin kasashe 23 ke fafutukar ganin ta cimma kason da ta ke da shi da wasu kasashe kamar Angola da Najeriya da ba za su iya habaka hanyoyin hako da man ba da sauransu kamar Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa ba.
A cikin watan Disamba, jimillar adadin albarkatun da OPEC ke fitarwa ya karu da ganga 90,000 a kowace rana, wanda haura 400,000 da ake son cimmawa, a cewar wani bincike na kamfanin dillancin labarai na Bloomberg.
Masana dai na ganin kasuwar ta kara samun habaka ne sakamakon tashe-tashen hankulan da suka addabi jiga-jigan kasashen da ke samar da mai, wato Rasha, Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa.
A ranar Litinin ne Hadaddiyar Daular Larabawa ta sake kakkabo wani makami mai linzami da ‘yan tawayen Huthi na Yaman suka harba, wanda shi ne hari na baya-bayan nan da aka kai wa kasar, wadda ke cikin kawancen sojan da Saudiyya ke jagoranta.
A Turai, zaman dar-dar tsakanin Rasha da kawayenta na Yamma ya kai matsayin mafi girma tun bayan yakin cacar-baka bayan da fadar Kremlin ta tara sojoji a kan iyakarta da Ukraine.