A karshe Peter Obi dan takarar shugaban kasa na Labour Party, LP, ya lissafa mafi yawancin matsalolin da Najeriya ke fama da su.
Dan takarar shugaban kasar ya ce yan Najeriya sun kasance suna zaben shugabannin da daga baya za su basu kunya.
Ya lissafa matsalolin da ke adabar kasar kamar rashawa, rashin kula da tattalin arziki, mika mulki ga wadanda ba su cancanta ba da sauran su.
Gabanin babban zaben shekarar 2023, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, a ranar Asabar, 19 ga watan Nuwamba, ya lissafa manyan matsalolin da Najeriya ke fama da su.
Obi ya bayyana hakan ne a sahihin shafinsa na Twitter. A cewarsa, galibin shugabannin da yan Najeriya ke zabar su a karshe sai da suka bata musu rai.
1. Shugabanni marasa nagarta.
2. Rashin tsaro.
3. Rashawa.
4. Rashin kula da tattalin arziki.
5. Mutanen da ba su cancanta ba suna rike da mukamai a matakai daban-daban na gwamnati.
6. Matsanancin talauci yayin da akwai yalwa.
Ya ce:
“Rikicin kabilanci da addini. Amma duk wadannan alamu ne. Muna ganin abin da ke faruw, amma matsalar na da zurfi.
Duk bayan shekaru hudu muna kokarin magance alamun ta hanyar zaben mutanen da suke cewa suna da mafita ga matsalolinmu.
Sannan kuma su bata mana rai.
“Dukanmu mun san matsalolin da muke fuskanta. Shugabannin marasa kyau. Rashin tsaro. Rashawa. Rashin kula da tattalin arziki. Mutane da ba su cancanta ba masu rike mukamai.
Matsanancin talauci.
“Makomar Afirka ta dogara ga Najeriya, kuma makomar Najeriya ta dogara da shugabanni masu nagarta.
Shugabannin kirki za su iya fitowa ne kawai daga mabiya nagari, wadanda za su rika bibiyar shugabannin da suka zaba.
Ya dogara gare ku.”
Mataimakin Shugaban Majalissar Dattijai Omo Ovie-Agege Yace Shine Ya Dakatar da Kudirin Tsige Shugaba Buhari
Shin kun gaji da wannan ƙasar? To, lokaci ya yi da za a dauki mataki.
Mu mayar da ofishin dan kasa mai wayayye a ofishi mafi girma a kasar.
Dalilai 5 Da Ka Iya Hana Peter Obi Cin Zaben 2023 – Fitch Solutions
Sabanin abinda ake radawa, bincike Fitch Solutions ya nuna cewa Peter Obi, dan takaran kujerar shugaban kasa na jam’iyyar LP zai sha kaye a zaben 2023.
A rahoton binciken da kamfanin Fitch Solutions ya fitar, ya bayyana dalilan da ya ika hana Peter Obi samun nasara a karshe.
Source:Legithausa