Jam’iyya mai kayan marmari wato NNPP tayi wani babban kamu a jihar Gombe, arewa maso gabashin Najeriya.
Ɗan takakar gwamna a jam’iyyar, Khamisu Mailantarki ya amshi dubunnan masu sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP.
Ya buƙace su da su cigaba da tallatawa da samarwa da jam’iyyar magoya baya a jihar gabanin 2023.
Ɗan takarar gwamnan jihar Gombe a ƙarkashin inuwar jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Khamisu Mailantarki, ya amshi dubunnan ƴaƴan jam’iyyar PDP.
Ɗan takarar gwamnan ya dai tarbi shugabanni da mambobin ƙungiyar Sardauna Dawo-Dawo, wacce take ta magoya bayan PDP.
Ya dai amshi waɗanda suka sauya sheƙar daga PDP zuwa NNPP a Gombe, a ranar Juma’a.
Rahoton jaridar The Punch ya tabbatar Jam’iyyar NNPP tayi babban kamu a jihar Gombe, ta amshi magoya bayan PDP.
Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Abdullahi Maikano, shine ya ƙarbe su a hukumance.
Ƙungiyar ta Sardauna Dawo-Dawo, ta sauya sunan ta zuwa tafiyar Mailantarki bayan sauya sheƙar inda take cewa ta yanke shawarar marawa ɗan takarar NNPP baya saboda mutum ne “matashi, ya cancanta, mai jini a jika da kirki.”
Shugaban ƙungiyar Muhammad Makson ya bayyana cewa: Ɓallewar mu daga goyon bayan PDP mataki ne wanda muka yanke a tare, dukkanin mu mun yanke shawarar tafiya sannan mu koma NNPP domin mu samu shugabanci mai kyau a jihar Gombe.
Mun aminta cewa Mailantarki yana da hali mai kyau da ƙwarewar da zai ceto jihar Gombe daga mulkin rashin kataɓus na APC. Mutum ne wanda a baya ya riƙa faɗin abubuwan da suka dace sannan yayi abubuwan da suka kamata.
Shugaban ya bayyana cewa ƙungiyar tana da shugabanni kusan 2000 da mambobi 20,000 a cikin mazaɓu 114 na jihar Gombe.
“Muna Faɗin Allah a Baki”
Mailantarki ya tabbatar musu da cewa za a riƙa damawa da su a dukkanin lamuran jam’iyyar.
Musamman yanzu da aka buga kugen yaƙin neman zaɓe, sannan Insha Allah, NNPP zata lashe babban zaɓe dake tafe.
Ya buƙace su da su cigaba da tattarowa jam’iyyar magoya baya sannan su tallata ƴan takarar ta a jihar.
A wani labarin kuma Gwamna Soludo na Anambra Ya gana da Atiku, ya faɗa masa yana cikin waɗanda zasu iya gaje Buhari a 2023.
Idan baku manta ba a watan Nuwamban da ya gabata, gwamnan yace mutum biyu ne ke neman shugaban ƙasa a 2023, sauran duk yan wasan kwaikwayo ne.
Atiku Abubakar ya ziyarci gwamnan har gidan gwamnati sa’ilin da jirgin yakinsa ya dira Anambra ranar Alhamis.