Shugaban kungiyar tsaro ta NATO, Jens Stoltenberg ya gayyaci Rasha da kawayenta na yankin arewacin Atlantika zuwa wata sabuwar tattaunawa domin kawar da zargin yiwuwar kai wa Ukraine hari.
A tattaunawarsa da manema labarai a Berlin, ya ce manufar ita ce, samar da mafita da kuma sake nazaratar bukatun Rasha, hadi da kokarin lalubo hanyar da za ta hana duk wani harin soji kan Ukraine.
A ranar Larabar da ta gabata ne Amurka da kawayenta na Turai suka tattauna da kasar Rasha wanda kungiyar tsaro ta NATO ta jagaoranata, zaman tattaaunawar da ba a sake haduwa ba tun shekarar 2019.
A yayin da yake jaddada bambance-bambancen ra’ayoyi da ke tsakanin bangarorin biyu, Stoltenberg ya ce, kasashe kawancen NATO a shirye suke don ci gaba da tattaunawa, amma Rasha ta kasa cimma matsaya kan shawarar sake zama a teburi.
A birnin Moscow, ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya ce, Rasha na jiran martani daga kasashen yammacin duniya game da kwararan bukatun tsaro da aka gabatar a tarurrukan da suka yi makon jiya kafin ci gaba da tattaunawa kan Ukraine.