Fitaccen masoyin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Sirajo Saidu Sokoto, ya sake jaddada kaunarsa ga shugaban kasan, inda ya tabbatar da cewa idan ba mutuwa ba babu abinda zai raba shi da buhari.
A wallafar da yayi a Facebook, ya sanar da cewa dattijon shugaban kasan yafi masu zaginsa gaskiya kuma mutuwa ce kadai ce zata raba su.
Sanannen masoyin shugaban kasan ya saba caccakar masu sukar Buhari duk da sace ‘yan uwansa maza 5 da ‘yan bindiga suka yi a Sokoto shekarar da ta gabata.
Idan za mu tuna, Sirajo Saidu Sokoto a shekaar da ta gabata ta yi bore tare da sanar da cewa baya tare da shugaban kasan bayan ‘yan bindiga sun yi awon gaba da ‘yan uwansa maza har biyar a jihar Sokoto.
Saidu fitaccen masoyin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne a kafara sada zumuntar zamani ta Facebook kuma an san ya kware wurin caccakar masu zukar shugaba Buhari da jam’iyyar APC.
A ranar Juma’a, 29 ga watan Yulin 2022, ya sake jaddada goyon bayansa da kauna ga shugaban kasan Muhammadu Buhari.
“Ka fi masu zaginka gaskiya dattijo. Mun yi alkawarin mutuwa ce kadai zata raba mu da Buhari,” ya rubuta.
A wani labarin na daban kuma rundunar sojin Rasha tare da ‘yan awaren da ke samun goyon bayan kasar sun zargi dakarun Ukraine da kai kari kan wani gidan yarin da ta garkame fursunonin yaki da take tsare da su a gabashin kasar, tana mai cewa gwammai sun mutu, da dama kuma sun samu raunuka.
Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce an kai har ikan gidan yarin da ake tsare da fursunonin yaki a yankin Donetsk da ke hannun ‘yan aware a gabashin Ukraine da rokoki samfurin HIMARS da aka kera a Amurka.
Sanarwar ta ce fursunonin yaki 40 ne suka mutu, a yayin da 75 suka jikkata, ta kuma kara da cewa ma’aikatan gidan yarin 8 sun samu raunuka.
An samu alkalumma masu cin karo da juna a game da wadanda suka mutu, inda a yayin da jagoran ‘yan awaren Donetsk, Denis Pushilin, ya ce mutane 47 ne suka mutu, rundunar mayakan ‘yan awaren ta Territorial defence forces ta ce 53 suka mutu.
Jimillar fursunonin yaki 193 ne ke tsare a wannan gidan yarin a lokacin da aka kai harin a cewar Putin yayin da yake jawabi ana watsawa kai tsaye a kafar sadarwa.
Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce fursunonin yakin yakin, wadanda ‘yan kasar Ukraine ne sun hada da dakarun bataliyar Azov wadanda suka kare wani yanki na na birnin Mariupol mai tashar jirgin ruwan.
A watan Mayu ne aka yi mayakan Ukraine 2500 kawanya bayan shafe makonni ana bata kashi birnin Mariupol.
Source:hausalegitng