Akalla mutane 10 suka rasa rayukansu sakamakon wani artabu tsakanin mambobin kungiyoyin asiri a jihar Osun da ke kudancin Najeriya kamar yadda Kamfanin Dillacin Labaran kasar ya rawaito.
Rahotanni sun ce, wata kungiya ce ta fara kai wa abokiyar gabarta farmaki a yankin Irojo a cikin daren ranar Talata, kafin daga bisani ita ma ta mayar da martini.
Wannan tashin hankalin ya tilasta wa mazauna yankin rufe shagunansu, yayin da al’umma suka yi lamo cikin gidajensu domin tsira da rayukansu, inda tituna da unguwanni suka kasance wayam babu kowa.
Bayanai na cewa, ana yawan samun irin wannan rikicin tsakanin kungiyoyin daba a jihar ta Osun mai dadadden tarihi a kasar Yarbawa, lamarin da ya sa jama’a ke rayuwa cikin fargaba a mafi tarin lokuta.
Tuni Sarakunan gargajiya na yankin suka tashi haikan, suna neman agajin hukumomin tsaro domin shawo kan wannan al’amari, yayin da a yanzu aka baza jami’an ‘yan sanda da na tsaron farin kaya.
Ya ce ‘yan sanda sun yi fito na fito da su ‘yan bindigar da ake zargi ‘yan kungiyaar IPOB ne, lamarin da ya sa suka tsere zuwa wani otel don neman mafaka, amma jami’an suka bi bayansu, inda suka kame 17 daga cikinsu.
Hari na biyu
Zalika, hari na biyun da ya auku a ranar Lahadi, wani kwantan bauna ne da ‘yan bindigar suka yi a jihar Anambra, inda suka kashe jami’an ‘yan sanda 2 daga cikin ayarin wani babban jammi’in gwamnatin jihar.
Samun karuwar hare-hare
Yankijn kudu maso gabashin Najeriya yana fuskantar hauhawar tashin hankali, inda a shekarar da ta gabata, ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan awaren Biafra ne suka kashe sama da ‘yan sanda 130 kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka ruwaito.
Fiye da mutane miliyan daya ne suka mutu a yakin basasa da aka shafe watanni 30 ana yi, bayan da a shekarar 1967 wasu sojoji daga ‘yan kabilar Igbo suka ayyana ‘yantatar kasar Biafra.