Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta Najeriya ta tsige mataimakin gwamnan jihar , Barista Mahdi Aliyu Gusau.
An zargi Gusau da yin amfani da karfin kujerar A wani zaman farko da ‘yan Majalisar suka yi a wannan Laraba, mambobi 20 daga cikin 24 sun kada kuri’ar amincewa da tsige mataimakin gwamnansa wajen aikata laifukan kamar yadda kwamitin binciken ya bayyana a cikin rahotonsa wanda aka mika wa shugaban Majalisar Dokokin Hon. Nasiru Mu’azu Magarya a yau Laraba.
Shugaban Majalisar ne ya karanta bayanan da ke kunshe cikin rahoton a zauren Majalisar Dokokin.
Gusau dai ya sha korafin cewa, yana fuskantar musgunawa daga gwamnan jihar, Bello Mutawalle sakamakon banbancin jam’iyya.
Tun bayan da gwamna Mutawalle ya sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC daga PDP, Gusau ya ki biye masa, yana mai cewa, yana nan daram a cikin jam’iyyar PDP, abin da wasu ke kallo a matsayin musabbabin bita-da kulli a gare shi.
A wani labarin na daban Hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta zargi kasashen China, Russia da Serbia da ci gaba da baiwa ‘yan tawayen kasar Myanmar muggan makaman da suke amfani da su wajen hallakawa da kuma azabtar da farafen hula.
A don haka Tom Andrew ya bukaci kwamitin tsaron da ya yi gaggawar jan hankulan wadannan kasashe don magance matsalar, da kuma kawo karshen yawon makamai a hannun farafen hula.
Wannan dai na cikin rahoton binciken da aka dade ana jira gada gareshi, kan inda sojojin ke samun makamai, wanda kuma ya bankado yadda bayan sojoji har ‘yan tawayen ke samun makaman.
A cewar sa dukannin kasashen Uku na baiwa ‘yan tawayen makaman ne da cikakken sanin cewa zasu yi amfani da su ne kan fararen hula, wanda kuma hakan take dokokin kasa da kasa ne.
Tun daya ga watan Fabrarirun bara, lokacin da sojoji suka hambarar da gwammnatin Aung San Su kyi ne kasar ta fada cikin mummunan tashin hankalin da ya tafi da rayukan mutane sama da dubu 1 da dari 5, yayin da ake tsare da fiye da dubu 12, sai sama da dubu 44 da suka bar muhallan su ala tilas.