Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta yi nasarar dage kofin kalubale na Carabao a daren jiya lahadi bayan lallasa Chelsea a bugun fenariti.
Mai horar da tawagar Chelsea Thomas Tuchel dai ya gamu da kakkausar suka saboda yadda ya sauya mai tsaron raga Edouard Mendy zuwa Kepa a kasa da minti 1 gabanin tafiya bugun na fenariti, duk da yadda Mendi ya doka mintuna 120 na wasan.
Tuchel dai na kallon Kepa a matsayin gwani ta bangaren bugun fenariti amma kuma sai ya bayyana ta hannunsa ne tawagar ta samu nakasu a jiyan kwatankwacin dai abin da ya faru a 2019 yayin haduwarsu da Manchester City.
Kofin na Carabao dai shi ne karo na 9 da zuwa yanzu Liverpool ta lashe, yayinda kuma ta ke harin kofunan Firimiya da na FA a wannan kaka.
Yayin wasan na jiya dai kungiyoyin biyu makwabtan juna a teburin Firimiya sun nuna goyon baya ga Russia da fafata yaki.
A wani labarin na daban Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya ce ya yi wuri a fara yiwa tawagarsa tunanin kamo takwararta Manchester City bayan nasararsu kan Crystal Palace da kwallaye 3 da 1 wanda ya rage tazarar da ke tsakaninsu da tawagar ta Pep Guardiola zuwa maki 9.
Acewar Jurgen Klopp bai fara sawa a ransa za su yi tsere da City a yanzu ba, abu mafi muhimmanci da ya fi mayar da hankali akai shi ne ganin sun yi nasara a dukkanin wasannin da ke tsakanin gabanin tsere ya fara tsakaninsu a watanni kalilan gabanin karkare gasar.
Liverpool dai na da wasa a hannu zuwa yanzu da aka dage saboda corona kuma tazarar maki 9 ke tsakaninta da Cityn dai dai lokacin da su ke shirin haduwa a Etihad cikin watan Aprilu karkashin gasar ta Firimiya.
A bangare guda rikewar da Brighton ta yi wa Chelsea a karawarsu ta jiya da aka tashi babu kwallo tsakaninsu ya rage barazanar da Liverpool ke fuskanta daga mai mataki ta 3 a teburin gasar inda a yanzu su ke da tazarar maki 1 amma kuma Chelsea ta doka wasa 24 ne sabanin 22 da Liverpool ta doka.