Rahotanni daga Najeriya na cewa an sace fasinjoji da dama bayan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai kan jirgin kasa da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a yammacin ranar Litinin, wanda yayi sanadiyar kashe ruyuka da jikkatar wasu.
Wani fasinja da yace a kan idon sa aka kashe wani na kusa da shi, yace sun ga gawar mutane akalla goma, yayin da akayi gurkuwa da mutane da dama.
Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraren rahotan waklin mu na Abuja n n Mohammed Sani Abubakar.
A wani labarin na dabaGwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El Rufa’i ya bayyana miyagun mutanen da ke baiwa ‘yan bindiga bayanai, a matsayin babban kalubalen da ke dakile yunkurin gwamnati na kawo karshen ta’addancin da ya addabi al’ummar jihar.
Gwamnan ya koka ne ranar Asabar a Kaduna, yayin bikin Ranar Tunawa da ’Yan Mazan Jiya ta Najeriya, wanda ake yi ranar 15 ga watan Janairun kowace shekara domin tunawa da ’yan Najeriya da suka sadaukar da rayuwarsu domin kare martabar kasar da al’ummarta.
A wata sanarwa da ta fitar kan batun tsaron, gwamnatin jihar Kaduna ta ce jami’an soji sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda uku, a yayin da suke sintiri a hanyar Telele-Sabon Gida a karamar hukumar Chikun da ke jihar.
A cewar sanarwar da Kwamishinan tsaron cikin gidan Kaduna Samuel Aruwan ya fitar, sojojin sun yi wa ‘yan bindigan kwanton bauna ne a wani wurin da ake zargin matattara ce ta ‘yan ta’adda da ke tafka ta’asa a kan hanyar ta Telele-sabon Gida.