Kamfanin wutar lantarki na jihar Kaduna TCN, ya katse duka layukan rarraba wutar lantarkin dake jihar domin bin umarnin ƙungiyar ƙwadugo.
Kamfanin yace ya zama waji ya yanke wutar kasan cewar dukkan ma’aikatansa na ƙarƙashin kungiyar ta NLC .
Wannan yajin aiki na zuwa ne biyo bayan korar da gwamnatin jihar Kaduna ta yi wa wasu ma’aikata kimanin 4,000 a jihar.
A yayin da ake gab da shiga yajin aikin gargaɗi na kwana biyar wanda ƙungiyar kwadugo ta bada umarni a jihar Kaduna, kamfanin rarraba wutar lantarkin jihar TCN ya katse duka layukan wutar jihar.
Kamfanin ya katse gaba ɗaya wutar ne a tsakiyar daren ranar Asabar biyo bayan gargaɗin da ma’aikatan wutar lantarki suka kaiwa kamfanin cewa ƙungiyar ƙwadugo ta basu umarnin shiga yajin aiki.
Rahoton Dailytrust ya bayyana cewa ƙungiyar ƙwadugo NLC, ta fara ƙoƙarin haɗa kan dukkan ma’aikatan jihar domin tabbatar da an dakatar da komai a faɗin jihar Kaduna.
Wannan wani ƙoƙari ne da ƙungiyar take yi domin tilasta wa gwamnatin Malam Nasir El-Rufa’i ta janye ƙudirinta na korar wasu ma’aikata a jihar.
A ranar Asabar gwamna El-Rufa’i ya kare matakin gwamnatinsa na korar ma’aikata inda yace gwamnatin sa ba zata cigaba da kwashe kuɗin da take samu ba wajen biyan Albashi.
Sai dai duk da haka bai hana TCN jefa mutanen jihar cikin duhu ba, inda kamfanin ya fitar da wani jawabi na musamman ga kwastomominsa yana mai shaida musu za’a samu matsalar samun wuta daga ranar Lahadi sakamakon yajin aiki da zasu shiga.
A sanarwar da kamafanin wutar lantarkin wanda shugaban yaɗa labarai ya fitar, yace: “Ya zama wajibi ga ma’aikatan mu su bi duk umarnin da Ƙungiyar ƙwadugo ta basu kasan cewar suna ƙaraƙashin ƙungiyar.”
“Bisa umarnin ƙungiyar ta ƙwadugo, kamfanin mu ya katse duka layukan wutar lantarki 33KV dake faɗin jihar nan ta Kaduna.”
A wani labarin kuma Rahoto Na Musamman: Yadda Jami’an Kwastam Suka Buɗe Wuta Ranar Sallah, Mutum 6 Suka Mutu Mutum 6 ne suka rasa rayukansu a wata musayar wuta da aka yi tsakanin hukumar kwastam da yan fasa ƙwauri a ƙauyen Iseyin jihar Oyo.
Matasan garin sun harzuƙa da kisan da akayi wa mutane waɗanda babu ruwansu a rigimar, inda suka lalata wasu motocin jami’an kwastam.