Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewar kasar ta shiga matakin karshe na yaki da kungiyar boko haram, yayin da ya sha alwashin murkushe su tare da yan bindigar da suka hana zaman lafiya a yankin arewa maso yammacin kasar.
Shugaban yace tuni ya bada odar sayo jiragen saman yaki da manyan makamai daga Amurka tare da motocin yaki wadanda za’a kaddamar da su akan irin wadannan mutane da suka hana zaman lafiya a Najeriya.
Buhari wanda ya baiwa sojoji umurnin afkawa ‘yan bindiga a jihohin Zamfara da Sokoto yace ba zasu ragawa wadannan mutanen ba, saboda irin illar da suke yiwa jama’a.
Shugaban kasar ya bukaci ‘Yan Najeriya da su yiwa gwamnatin sa adalci, lura da yadda suka samu kasar lokacin da suka karbi mulki da kuma yadda take ayau.
Buhari yace mutanen arewa maso gabas sun fi kowa sanin halin da ake ciki lokacin da ya karbi mulki, kuma sun bayyana haka wajen irin tarbar da suka masa.
Shugaban yace da zaran wa’adin mulkin sa ya kare zai sauka daga karagar mulki kamar yadda yayi alkawari lokacin da ya rantse da Al Qur’ani cewar zai mutunta kundin tsarin mulki, saboda haka nan da watanni 17 da ikon Allah zai sauka daga mulki domin baiwa wanda zai gaje shi damar dorawa daga inda ya tsaya.
Sai dai Kungiyar Tintiba ta Arewacin Najeriya da ake kira ACF ta zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da koyawa gwamnonin arewacin kasar nuna halin ko-in-kula dangane da hare haren da ake kaiwa jama’ar yankin ana kashe su a ba tare da nuna wata damuwa ba.
Yawe yace abinda jama’a ke gani daga shugabannin na nuna cewar sun damu da rayuwar su ce kawai tare da ta iyalan su, amma ba na jama’ar da suke yiwa shugabanci ba.
Sanarwar tace banda Gwamnan Borno Babagana Zulum wanda koda yaushe ke kan hanyar zuwa wajen jama’ar da yake yiwa shugabanci duk lokacin da aka kai musu hari, shugaban kasa Buhari tare da sauran gwamnonin arewacin kasar basu damu da ziyarar wadanda iftila’i ya afka musu ba, ballanta su jajanta musu.
Yawe yace kungiyar ta gabatar da rashin amincewar ta da kuma fushin ta dangane da abinda ta kira amincewa da ci gaba da kashe fararen hula ba tare da kaukautawa ba daga bangaren shugabannin.
Kungiyar tace ko a jiya lahadi ‘Yan bindiga sun hallaka mutane 38 a karmar hukumar Giwa dake Jihar Kaduna, kuma basu ga dalilin da ya hana shugaban kasa Buhari da gwamnan jihar Malam Nasir El Rufai ziyarar inda aka kai harin domin jajanta musu ba.
Yawe ya bada misali akan Gwamna Zulum na Jihar Borno wanda a kwanakin nan ya tashi zuwa Askira Uba domin jajantawa mutanen yankin bayan harin da ya hallaka mutane 10.
Yawe yace mutanen da suke fuskantar wadannan hare hare a yankin arewacin Najeriya sun yanke yakinin cewar babu wanda ya damu da rayuwar su.