Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta/na gudanar da babban taronta na kasa domin zaben sabon shugabanta tare da shawo kan rikicin cikin gidan da take fama da shi, kafin daga bisani a kai ga zabar wanda zai maye gurbin shugaba Muhammadu Buhari a zaben shekarar 2023.
Rahotanni sun ce Sanata Adamu dai shi ne dan takarar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke marawa baya.
Sa’o’i kadan kafin fara gudanar da babban taron jam’iyya mai mulkin Najeriyar ta APC, babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ta shigar da kara gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda take kalubalantar tsarin mulkin APCn, tare da neman a bayyana taron na ta a matsayin wanda ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.
PDP, ta kuma bukaci kotun da ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya, ta soke rajistar jam’iyyar APC.
Cikin karar da ta shigar, PDP ta yi ikirarin cewa dukkanin tsarin APC ya sabawa kundin tsarin mulki na tafiyar da jam’iyyar siyasa.
A wani labarin na daban kuma Yayin da zaben shekarar 2023 ke kara karatowa a Najeriya, Babbar Jam’iyyar adawar kasar ta PDP na cigaba da fuskantar matsalolin cikin gida inda wasu daga cikin jiga jigan ‘yayan ta ke ficewa suna komawa Jam’iyyar APC mai mulki.
Rahotanni sun ce Ayade ya bayyana sauya shekar ne bayan ganawar da yayi da wasu takwarorin sa a birnin Calabar da suka kunshi shugaban Gwamnonin kasar Kayode Fayemi na Jihar Ekiti da shugaban Gwamnonin Arewa Simon Lalong da Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodinma da kuma takwaran san a Jigawa Abubakar Badaru tare da shugaban Jam’iyyar na riko Mai Mala Buni, Gwamnan Jihar Yobe.
Wannan na zuwa ne bayan sauya shekara da Gwamnan Ebonyi David Umahi yayi daga PDP zuwa APC, yayion da takwaran sa na Edo Godwin Obaseki ya bar APC zuwa PDP lokacin da ta hana shi tsayawa takarar wa’adi na biyu.