Gamayyar jami’an tsaron wata runduna ta musamman a Jihar Neja ta hallaka ’yan bindiga da dama da suka addabi Kananan Hukumomin Shiroro da Munya da ke Jihar.
Kwamishinan Kananan Hukumomi, da Tsaron Cikin Gida na Jihar, Emmanuel Umar, yace dabbobin da aka ceto sun hada da shanu sama da 300 da tumaki sama da 100, wanda za su kasance karkashin kulawar Ma’aikatar Kula da Dabbobi ta Jihar.
A wani labarin na daban kuma Mazauna unguwar Mareri Quarters da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara sun fita daga unguwar sakamakon tsoron hari daga ‘yan bindiga.
Mazauna Unguwar ne suka sanar da ‘yan sintiri kan batun sace Papa da iyalansa, su kuma ba su yi wata wata ba suka shiga aikin ceton su.
Bayan da suka ceto su ne, suka sanar da jami’an tsaro, wanda suka datse hanyoyin fita ga su ‘yan bindigan, lamarin da ya sa aka kashe 6 daga cikin barayin.
Wani mazaunin Unguwar ya ce akasarin makawaftansa ba sa kwana a gidajensu tun bayan aukuwar lamarin, don gudun abin da ‘yan bindigan ka iya aiwatarwa a matsayin ramuwa.