Iyalan fasinjojin jirgin kasan da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su bayan harin da suka kai musu akan hanyar Abuja zuwa Kaduna, sun roki shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ya ceci iyalai, ‘yan uwa da abokan nasu, ta hanyar gaggauta amsa bukatar maharan na sakar musu ‘yan uwansu 8 da ke hannun jami’an tsaro.
Iyalan fasinjojin sun bayyana haka ne, yayin zanga-zangar lumanar da suka yi da safiyar Larabar nan, a cigaba da kokarin jan hankalin gwamnatin Najeriya domin ceto ‘yan uwan nasu.
Masu zanga-zangar sun bayyana damuwa kan barazanar da ‘yan ta’addan suka yi na kashe baki dayan mutanen da suka yi garkuwa da su nan da kwanaki bakwai, idan har gwamnatin Najeriya ba ta sakar musu ‘yan uwansu. yara 8 da ake tsare da su a jihar Adamawa ba.
Akalla fasinjojin jirgin kasan da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna 61 ne suka shafe kusan watanni 2 a hannun ‘yan bindigar da suka kai musu farmaki a cikin watan Maris, inda suka dasa bam a kan titin jirgin kasan, daga bisani kuma suka bude wuta.
A wani labarin na daban matsalar ayyukan ta’addanci dake karuwa a kasashen Afirka tare da juyin mulkin da sojoji ke yi wajen kawar da zababbun shugabanni na daga cikin manyan batutuwan da shugabannin kasashen Afirka zasu mayar da hankali akai wajen taron sun a musamman da ke gudana a Equatorial Guinea a wannan juma’a mai zuwa.
Shugaban gudanarwar kungiyar Moussa Faki Mahamat Tashe tashen hankulan dake nasaba da ayyukan ta’addanci sun karu daga Libya zuwa Mozambique da kuma daga Mali zuwa Somali, yayin da matsalar ke neman zama ruwan dare a Yankin Sahel da Tafkin Chadi da kuma Gabashin Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo.
Dangane da juyin mulkin soji kuwa da aka gani na baya bayan nan a kasashen Mali da Guinea da Burkina Faso da kuma Sudan, shugaban gudanarwar kungiyar yace matsalar ta taimaka wajen mayar da hannu agogo baya dangane da shirin dimokiradiya.
Sojoji na jan kafa wajen shirya zabe – Mahamat
Mahamat ya kuma bayyana damuwa da tsaikon da ake samu a tsakanin wadannan kasashe wajen gabatar da shirin gudanar da zabe da zummar dawo da shugabannin fararen hula.
Kungiyar kasashen Afirka ta AU da ECOWAS da kungiyar kasashen Turai da Amurka da kuma Majalisar Dinkin Duniya duk sun bayyana damuwa da jinkirin mayar da mulkin fararen hular a wadannan kasashe, yayin da wasu daga cikin su suka sanya takunkumin karya tattalin arziki akan sojojin da suka kifar da gwamnatin.
Ana saran taron ya kuma tattauna matsayin Chadi wadda ke da shugaban soji Mahamat Idris Deby, wanda ya maye gurbin mahaifin sa da kuma Nazari akan alkawarin da yayi na gudanar da zabe bayan watanni 18.