Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kai samame kan wata masana’antar har-hada bamabamai a yankin Imo, kudu maso gabashin kasar inda ake ta samun tashe-tashen hankula na ‘yan aware.
Abattam ya ce sun samu nasarar ce bayan samun bayanan sirri kan maboyar da ‘ya’yan haramtacciyar kungiyar IPOB da kuma na kungiyar ESN ke kera bama-baman da suke amfani da su wajen kai hare-hare kan ofisoshin ‘yan sanda da cibiyoyin gwamnati a jihar ta Imo.
Kakakin ‘yan sandan y ace tuni mutumin ya amsa laifinsa kuma yana cigaba da basu hadin kai wajen gudanar da bincike.
Wata kididdiga ta nuna cewar a shekarar da ta gabata kadai ‘yan sanda da wasu jami’an tsaro akalla 130 ko sama da hakan suka rasa rayukansu, a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya sakamakon. hare-haren ‘yan awaren IPOB.
A wani labarin na daban Fargaba ta mamaye mazauna yankin kudu maso gabashin Najeriya sakamakon jerin hare haren da ake zargin mayakan haramtacciyar kungiyar IPOB ke kai wa jami’an tsaro wanda ya yi sanadiyar kashe ‘yan sanda 127 a cikin wannan shekara.
Rahotanni sun ce tun bayan kaddamar da hari kann cibiyar ‘yan sandan Jihar Imo a ranar 5 ga watan Afrilu sakin firsinoni kusan 2,000 an samu hare hare kusan 30 a Ofisoshin ‘yan sandan da ke yankin baki daya.
Wannan ya sa jami’an ‘yan sandan da ke yankin basa iya sanya kayan Sarki domin zuwa wurin aikin su, yayin da yan bindigar dauke da makamai ke bin su har zuwa ofisoshin su suna kai musu hari.
Yayin da wasu ke danganta hare haren da shirin zaben shekarar 2023 da za’ayi domin maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari wasu na danganta shi da masu aikata laifuffuka dake fakewa da sunan masu fafutukar kafa kasar Biafra.
Akalla tashohin Yan Sanda 5 dauke da kayan aiki aka bankawa wuta a yankin, abinda ke jefa fargaba dangane da shirin zaben mai zuwa.
Ita dai kungiyar IPOB ta nesanta kan ta daga wadannan hare hare da suka haifar da rasa rayuka da kuma asarar tarin dukiya.
Wannan yankin yayi asarar akalla mutane miliyan guda lokacin da aka kwashe watanni 30 ana fafata yakin basasan da ya fara daga watan Yulin shekarar 1967 lokacin da shugaban Yan aware Emeka Odumegwu-Ojukwu ya bayyana ballewar sa daga Najeriya.
Shugaban rundunar Yan Sandan Najeriya Usman Baba yace sun kama mutane akalla 600 da ake zargin suna da hannu wajen kai hare haren tare da kwace tarin makamai.