Lauyan nan na Kano, Abba Hikima Fagge, ya bukaci Gwamnatin Kano da ta duba Allah ta tsayar da aikin gadojin da ta kuduri aniyar yi a Kano ta hanyar ɗibar kudaden kananan hukumomi don gina gadoji a birni alhali kauyuka na cikin matsanancin hali da bukatar aiki.
Abba Hikima ya bayana hakan a shafinsa na Facebook a safiyar ranar Laraba inda mabiyansa ke ci gaba da bayana tsokacinsu kan kalaman nasa.
Hikima ya ce, “Irin wadannan abubuwan da ake dauko wa ke sawa mutane suke daukar gaba daya ashe ‘yan siyasa irinsu daya, ”
“Yanzu saboda Allah ina adalci anan? Kauyukan Kano suna cikin mugun hali, kwanaki Freedom Radio ta yi ta bankado matsalolin kauyukanmu amma a dauko kudinsu a saka a gada guda daya Me wannan kudin?”
“Lallai akwai wani abu da yake faruwa a kasa.” cewar Abba Hikima.

Source: LEADERSHIPHAUSA