Mataimakiyar shugabar Amurka kamala Harris zata ziyarci Paris dake kasar Faransa domin bunkasa shirin sasanta kasashen biyu wanda shugaba Joe biden da Emmanuel Macron suka fara, sakamakon rikicin kwangilar gina jiragen yakin karkashin tekun Australia da suka karbe daga Faransa.
Ziyarar Harris zata kunshi wasu manyan jiga jigan gwamnatin Amurka da suka hada da Sakataren harkokin wajen Antony Blinken da mai baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro Jake Sullivan.
Shugaba Biden ya gana da Macron a ranar juma’ar da ta gabata a birnin Rome wajen taron kungiyar G20, inda suka kawar da rashin jituwar dake tsakanin kasashen biyu, sakamakon soke kwangilar da Australia ta kulla da Faransa wadda ta mikawa kasar Amurka ta biliyoyin daloli.
Mataimakiyar shugabar zata gana da shugaba Emmanuel Macron a ranar laraba a fadar Elysee inda zasu tattauna batutuwa da dama da suka hada da dangantakar kasashen biyu da tsaron nahiyar Turai da yankin India da Pacific da kuma annobar korona.
Wani jami’in gwamnatin Amurka yace Harris zata halarci wani bikin karrama tsoffin sojojin Amurka da suka taka rawa a yakin duniya na farko da aka yi a shekarar 1918 wanda ake gudanar da hutu akai a kasar Amurka kowacce ranar 11 ga watan Nuwamba.
Sanarwar tace a ranar 12 ga wata, mataimakiyar shugabar zata wakilci Amurka a taron kasashen duniya domin taimakawa kasar Libya wanda za’a yi a Paris kafin zaben watan Disamba da kuma taron zaman lafiyar Paris da shugaba Emmanuel Macron zai jagoranta.