Gwamnatin Taliban da ke mulki a Afghanistan, ta bukaci kasashen musulmi da su kasance na farko da za su amince da ita, wanda hakan zai bai wa sauran
kasashen duniya damar ci gaba da bai wa kasar taimako a cewarta.
Majalisar ta ce ya zama dole a tabbatar kudade sun ci gaba da gudana cikin Afghanistan duk da cewar ba a san hakan ya zama taimako kai tsaye ga mayakan Taliban.
A taron manema labaran da ya gabatar jiya laraba, firaministan kasar Mohammad Hassan Akhund, ya ce duk wani taimako da kasashen duniya za su bai wa Afghanistan ba wai zai je ne a aljiuhun ‘yan Taliban ba, sai dai domin amfanin al’ummar kasar.
A wani labarin na daban Gwamnatin Taliban a Afghanistan ta gargadi kasashen Turai da Amurka game da matakan da su ke dauka na sanya mata takunkuman karya tattalin arziki wanda kungiyar ke cewa zai kara matsalar tsaro baya ga kara yawan ‘yan ciranin da za su kwararu kasashen nasu.
A watan Agustan da ya gabata ne, Taliban ta hambarar da gwamnatin Ashraf Ghani mai samun goyon bayan Amurka wanda ya kawo karshen rikicin shekaru 20 da Afghanistan ta yi fama da shi baya ga mayar da kasar turbar mulkin gargajiya bisa tsarin addinin Islama, sai dai matsalolin rashin kudin shiga sun dabaibaye kasar ta yankin Asiya musamman bayan kullemata asusun ajiyar da manyan kasashen suka yi da kuma katse tallafin da ta ke samu.
Ka zalika kokarin Taliban na dawo da zaman lafiya a kasar na fuskantar babbar barazana daga mayakan IS baya ga matsalar tattalin arziki da ke ci gaba da tsananta sakamakon takunkuman manyan kasashen Duniya akan kasar wanda ya haddasa karanci kudi a ilahirin bankunan Afghanistan.
Acewar ministan wajen na Afghanistan ta bakin kakakinsa, yayin zantawar ta su ta Doha matukar kasashen duniyar na bukatar zaman lafiyarsu, akwai bukatar su kawo karshen takunkuman kan Afghanistan wanda zai bata damar tafiyar da harkokinta musamman al’amuran da suka shafi tattalin arziki.
Muttaqi ya roki kassahen su bai wa Afghanistan damar tafiyar da harkokin kudi a bankuna baya ga sahale ayyukan agaji don ceto kasar daga durkushewa.
Turai dai na da fargabar karuwar kwararuwar ‘yan cirani idan har tattalin arzikin Afghanistan ya rushe wanda ya sa ta ke shirin matsa kaimi ga makwabtanta da suka kunshi Pakistan da Iran don su tsaurara matakn tsaro a iyakokinsu.