Gwamnati ta tabbatar da cewa akalla mutane 200 ‘yan bindiga sun kashe tare da raba wasu dubbai da muhallansu, yayin munanan hare-haren da suka kai cikin makon jiya a Jihar Zamfara da ke yankin arewa maso yammacin kasar.
A ranar Asabar din da ta gabata ne dai i, wasu mazauna yankunan da lamarin ya rutsa da su, suka shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, akalla mutane 140 ‘yan bindigar suka kashe a tsakanin ranakun Laraba zuwa Alhamis.
Ko da yake a na ta bangaren gwamnati a Jihar Zamfara ta bayyana adadin mamatan ne akan mutane 58, bayan da Sarkin Anka ya ce mutane 22 aka kashe a yankinsa, yayin da Sarkin Bukkuyum ya sanar da mutuwar wasu 36, alkaluman da kakakin gwamnatin Zamfara Zailani Bappa ya tabbatar a wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar Asabar.
Ranar Asabar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ya yi A-wadai da hare-haren ta’addancin a Zamfara, da ya bayyana a matsayin huce fushi kan wadanda basu ji ba basu gani ba, da ‘yan bindigar suka yi, saboda hare-haren da jami’an tsaron suka kaddamar akansu a baya bayan nan.
Wasu majiyoyi sun ce, daruruwan ‘yan ta’addan da suka kaddamar da munanan hare-haren, masu biyayya ne da kasurgumin dan fashin dajin nan Bello Turji, wadanda hare-haren jiragen yakin sojin Najeriya ya tilastawa tserewa daga sansanoninsu da ke dajin Fakai a karamar hukumar Shinkafi.