Gwamnan sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya janye dokar hana fita da ya kafa a cikin birnin Sokoto, matakin da ya ce ya fara aiki nan take, inda ya kuma haramta duk wani nau’i na gangami, ko jerin gwano a jihar har sai abinda hali yayi.
Gwamnan ya ce matakin ya biyo bayan tuntubar juna da hukumomin tsaro da abin ya shafa.
An dai kafa dokar hana fita ta sa’o’i 24 a birnin Sokoto ne bayan wata zanga-zanga da ta yi sanadin mutuwar mutum daya a jihar, kamar yadda wakilinmu ya tabbatar, yayin da wasu da dama suka jikkata a yayin zanga-zangar da ta janyo kafa dokar hana fitar a birnin Sokoto da kewayensa.
Masu zanga-zangar sun nemi sakin mutane biyu da ake zargi da kashe Deborah Samuel, bisa tuhumarta da batanci ga Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi.
A wani labarin na daban Majami’ar Katolika ta Holy Family a jihar Sokoto da ke Najeriya ta ce babu wanda aka kashe a yayin harin da wasu matasa Musulmi suka kai wa cocin a jiya Asabar.
Wata sanarwa da ta sami sa hannun daraktan watsa labarai na majami’ar, Christopher Omotosho ta ce sai dai masu zanga zangar sun lalata wani sashi na majami’ar, da kuma wani coci a cikin Sokoto.
Sanarwar ta ce masu gadin majami’ar sun dakile masu zanga zangar kafin su aikata barna dayawa.
Matasa da suka fusata ne suka bazama titunan Sokoto, inda suke zanga zangar neman a saki wadanda aka kama sakamakon zargin su da ake musu na kisan wata daliba da ta yi batanci ga Annabi Muhammad Tsira da Aminci Allah su tabata a gare shi.
A kokarinta na samar da sauki ga al’ummar jihar, gwamnatin Sokoto ta ayyana dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 24 a kwaryar jihar.