A wata sanarwa da ofishin Jagoran ya fitar a ya ce a bikin da za a gudanar gobe talata a Husainiyar Imam Khumaini da ke gidan Jagoran, Ayatullah Khamenei zai ba wa Sayyid Ra’isi takardar amincewarsa da zaɓan da aka masa a matsayin shugaban ƙasar Iran.
Sanarwar ta ƙara da cewa a gobe yayin bikin wanda zai samu halartar wasu daga cikin manyan jami’an ƙasar, ministan cikin gida na Iran ɗin zai gabatar da rahoto kan zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Yuni, daga nan kuma za a karanta abin da takardar kama aikin ta ƙumsa sai kuma jawabin da sabon shugaban da kuma Jagoran za su yi.
Bikin miƙa takardar amincewa da shugabancin dai shi ne mafarin kama aiki duk wani shugaban ƙasa da aka zaɓa a Iran, kuma an tabbatar da cewa gobe za’a gabatar dashi.
A ranar Alhamis, kwanaki biyu bayan wannan bikin ne dai ake sa ran Sayyid Ibrahim Ra’isin zai gudanar da rantsuwar kama aiki a hukumance a gaban ‘yan majalisar dokoki na Iran ɗin wanda hakan ke nufin kawo ƙarshen gwamnati mai ci yanzu da kuma fara aikin sabuwar gwamnatin.
A wani labarin na daban daga kasar masar shafin jaridar Sadl Balad ya bayar da rahoton cewa, a jiya Allah ya yi wa sheikh Khamis Jabir Saqar babban malamin kur’ani a kasar Masar rasuwa yana da shekaru 68 a duniya.
An haifi shehin malamina shekara ta 1953 a garin Damnahur ad ke cikin gundumar Buhaira a kasar ta Masar.
Ya yi karatua wajen manyan malamai na lokacinsa, kafin daga bisani kuma ya shiga jami’ar Azhar, inda a cikin kankanin lokaci ya shahara a cikin jami’ar saboda kwazonsa.
Ya koma ya ci gaba da karantawa a jami’ar Damnahur a bangaren addini, kafin daga bisani kuma ya zama shugaban bangaren bincike kan rubutattun kur’anai a jami’ar Azhar a tsakanin shekarun 2003 zuwa 2007.
Sheikh Jabir Saqar cibiyar azhar ta nada shi a matsayin babban daraktan cibiyar kula da lamurran kur’ani na lardin Buhaira baki daya, kuma ya rasu yana a kan hakan.