Rahotanni daga babban birnin tarayyar buja suna nuni da cewa gobara ta tashi hedikwatar ma’aikar kudin gwamnatin tarayya.
Babu tabbacin dalilin tashin gobarar amma dai tuni ma’aikatan kashe gobara suka isa wurin domin kashe gobarar.
Lamarin da jama’a da dama suka shiga bayyana ra’ayoyin su dangane da barkewar wannan gobara inda da dama suka bayyana cewa a kwai wata makarkashiya dangane da wannan gobara.
Jaridar Punch ta rawaito mai magana da yawun ma’aikatar kashe gobara Abraham Paul yana cewa ma’aikatan su suna bakin kakarin su domin tabbatar da cewa su kahse wanna gobara.
Sai dai kuma a wani sako da ma’aikatar kudin ta wallafa a shafin ta na tuwita ta tabbatar da cewa wannan gobara batayi munin da ake ta yadawa a kafafen sada zumunta ba inda ta bayyana cewa gobarar ta shafi wani bangare ne na zauren kasa dake ginin ma’aikatar kudin ta najeriya.
Amma sai dai ‘yan anjeriya da dama basu gamsu da wanna bayani ba inda suke zargin lallai a kwai wani lamari da ake so ab boye shine aka kirkiri wannan gobarar domin badda samu.
A wani labarin na daban shugaban kasar jamhuriyar musulunci ta Iran Sayyid Ibrahim Ra’esi ya bayyana aniyar gwamnatin sa na bude ofishin jakadanci a babbanbirnin qatar watau Doha.
A yayin da yake tattaunawa da manenma labarai bayan ziyarar kwana biyu daya gabatar a kasar ta Qatar Shugaba Ibrahim ra’esi ya bayyana hakan matsayin wani mataki da gwamnatin sa ta dauke domin kawar da rashin fahimta gami da habaka tattalin arziki tsakanin kasashen biyu makotan juna.
A yayin ziyarar tasa sarkin qatar da kuma shugaban kasar Iran sun rattaba hannu a kan wasu yarjejeniyoyi guda 14 gami da tattauna yadda za’a habaka sanya hannun jari tsakanin kasashen biyu gami da tattauna yadda za’a hade Iran da da Qatar din ta hanyar wani bututun karkashin ruwa.