Daruruwan matasa ne suka gudanar da gangami a Gashua dake Jihar Yoben Najeriya domin nuna goyan bayan su ga bukarar shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawal wanda ke neman Jam’iyyar APC ta sashi a gaba a matsayin ‘dan takarar shugaban kasa mai zuwa.
Matasan na gashua dauke da hotunan ‘dan takarar sun yi tattaki a cikin manyan titunan birnin domin nuna sha‘awar su ta ganin Sanata Lawal ya samu nasarar zaben fidda gwanin da za’ayi a karshen wannan mako wanda ya kunshi mutane sama da 20.
Daya daga cikin matasan Bukar A. Bukar yace Shugaban Majalisar Dattawan na da duk kwarewar da ake bukata domin tsayawa takara, musamman kishin kasa da kuma jajircewa wajen ganin ‘yan Najeriya sun samu zaman lafiya da walwala.
A fadar Sarkin Bade Alhaji Abubakar Umar Suleiman, daya daga cikin shugabannin matasan Hassan Bulama ya shaidawa Basaraken cewar matasan sun shirya gangamin ne domin bayyana goyan bayan su ga shugaban Majalisar Dattawan na ganin ya samu shugabancin Najeriya saboda yadda ya samar da ci gaba a yankin da kuma kasa baki daya.
Sanata Ahmed Lawal na daya daga cikin ‘yan takara na gaba gaba a zaben fidda gwanin da zai gudana a karshen wannan mako wanda ya kunshi ‘Yan takara irin su mataimakin shugaban kasa Yemo Osinbajo da Jagoran APC Bola Ahmed Tinubu.