‘Yan darikar Tijjaniya a Nigeria sun yiwa ‘dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu addu’ar samun nasara.
A wani taron zikirin kasa da maulidi da darikar ta shirya a garin Minna na jihar Neja, ta tabbatarwa da Tinubu matsayin uban darikar a Nigeria.
A wata sanarwa da sakataran yada labaran gwamna jihar Niger ya fitar kuma jaridar.
The Cable ta samu yace wanan zikirin wani bangare na maulidin da darikar Tijjaniya mai suna Ansarul Deeni Attijaniya ta shirya.
Inyass yace dan takarar jam’iyyar APC yardajjen mutum ne a bangarori da dama da suka hada da gina ‘dan adam, bunkasa abubuwan more rayuwa, sannan zai ci gaba da yin haka in aka zabeshi a matsayin shugaban kasa.
Shehin darikar ya ya roki al’ummar musulmi su ci gaba da addu’a dan ganin zaman lafiyar Nigeria.
A yayin taron zikirin akwai gwamnan jihar Niger, Kano, da karamin ministan harkokin kasar waje, da srakunan gargajiya da kuma tsohon kakakin majalisar wakilai Dimeji Bonkole.
A wani labarin kuma Gwamna Soludo na Anambra
Ya gana da Atiku, ya faɗa masa yana cikin waɗanda zasu iya gaje Buhari a 2023.
Idan baku manta ba a watan Nuwamban da ya gabata, gwamnan yace mutum biyu ne ke neman shugaban ƙasa a 2023, sauran duk yan wasan kwaikwayo ne.
Atiku Abubakar ya ziyarci gwamnan har gidan gwamnati sa’ilin da jirgin yakinsa ya dira Anambra ranar Alhamis.