Bukatun da Rasha ta gabatar kan rikicinta da Ukraine, a cikin mintunan karshe na tattaunawar ta da wasu manyan kasashen duniya, sun yi barazanar kawo cikas ga shirin farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran a ranar Juma’a, abinda ya sanya kungiyar EU sanar da dakatar da tattaunawar.
A karshen watan Nuwamba aka fara tattaunawar da ake yi a Vienna babban birnin kasar Austria tsakanin kasashen Birtaniya da China da Faransa da Jamus da Iran da kuma Rasha inda Amurka ta tura wakilci.
A makon da ya gabata Rasha ta ce tana neman a ba ta tabbacin cewa takunkumin da kasashen yamma suka kakaba wa tattalin arzikin ta bayan mamayewar da ta yi wa Ukraine ba zai shafi kasuwancinta da Iran ba.
A wani labarin na daban kuma Shirin nukiliyar Iran ya sake daukar hankali a daidai lokacin da kasar ta shiga sabuwar tattaunawa da manyan kasashen duniya a yau Litinin a birnin Vienna da zummar farfado da yarjejeniyar da suka cimma a shekarar 2015.
A karkashin yarjejeniyarsu ta shekarar 2015, Iran da manyan kasashen duniya da suka hada da Birtaniya da Faransa da Jamus da China da Amurka da Rasha sun amince cewa, Tehran ba za ta habbaka sinadarinta na Uranium fiye da kashi 3.67, adadin da ya yi kasa da kashi 90 da aka gindaya kafin fara amfani da makamin nukiliya.
Sai dai tun a cikin watan Mayun shekarar 2019, Iran ta sanar da karya ka’idojin yarjejeniyar da ta cimma da manyan kasashen, a matsayin martani ga tsohon shugaban Amurka Donald Trump wanda ya janye daga yarjejeniyar a 2018 tare da kakaba wa kasar takunkumai.
Wani rahoton baya-bayan nan da Hukumar da ke Sanya Ido kan Makamashin Nukiliya ta Duniya ta fihtar ya ce, a yanzu, Iran ta tattara karikitan nukiliya har kilogram dubu 2 da 489.7.
Kazalika Iran din ta fara samar da karafen uranium wanda daya ne daga cikin abubuwan da ake har-hadawa domin kera makaman nukilya kamar yadda Abdrea Stricker, wani masani a wata cibiyar kimiya ta birnin Washington ya fallasa.
A karkashin yarjejeniyar ta 2015, Iran dai ta yi alkwarin cewa, ba za ta samar da irin wannan karfe na uranium ba.