Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya roki ‘yan Najeriya su yi hakuri su zabi Bola Ahmed Tinubu a watan nan.
Yayin ralin APC a jihar Katsina ranar Litinin, Buhari ya ce Tinubu zai gyara kuskuren gwamnatinsa ya ɗora daga inda ya tsaya.
A ‘yan makonnin nan dai siyasa ta ɗau zafi a Najeriya musamman kan batun sauya takardun kuɗi da karancin Fetur.
Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya roki ɗaukacin ‘yan Najeriya da su yafe wa gwamnatinsa kuma su jure wa radadin da ta kawo masu.
Buhari ya kuma tabbatar da cewa gwamnati mai zuwa ta Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban ƙasa a inuwar APC, zai gyara kura-kuran kuma ya ɗora daga inda ya tsaya.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Buhari ya yi wannan furucin ne ranar Litinin yayin da yake jawabi ga dubannin masoya da magoya baya a filin kwallon Dikko Stadium Katsina.
A wurin Ralin APC na jihar Katsina, wanda ya gudana a filin kwallon Dikko, Buhari, ya dora laifin halin da ake ciki kan faɗuwar tattalin arziki sakamakon annobar cutar Korona.
Duk da haka a cewar shugaban ƙasan, gwamnatinsa ta kawo ci gaba kuma ta samu nasarori na zamani a tsawon lokacin da ta kwashe a kan mulki.
A kalamansa, Buhari ya ce: “Da sunan Allah, ina rokonku Dan Allah ku ƙara hakuri da mu kuma ku yafe mana. Ku faɗawa abokanku, ‘yan uwa maza da mata da ‘ya’yanku su ci gaba da jefa wa APC kuri’unsu.”
“Ku tabbata kun zaɓi Tinubu a matsayin shugaban kasa, Dikko Raɗɗa a matsayin gwamnan jihar Katsina da sauran ‘yan takarar jam’iyyar APC.”
Da yake jawabi, gwamna Aminu Bello Masara ya raba yakin neman zama shugaban ƙasa gida biyu, haske bisa wakilcin Tinubu na APC da duhu watau sauran yan takara.
Bayan haka ya sanar da cewa Tinubu ya ba da tallafin naira miliyan N100m ga iyalai da sauran mutanen da harin ‘yan ta’adda ya shafa a ƙaramar hukumar Bakori, This Day ta rahoto.
A wani labarin kuma Bola Tinubu ya yi karin haske game da tsamin alaƙarsa da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari Dan takarar shugaban ƙasan ya bayyana cewa duk masu ƙulle-kulle da tuggun ganin alaƙa tai tsami tsakaninsa da Buhari zasu ji kunya.
Tsohon gwamnan Legas ɗin ya kuma bayyana cewa Buhari yana bin tsarin mulkin Demokuradiyya duk da ya kasance tsohon soja.
Source:LegitHausa